Fatima bint al-Munzir bn al-Zubayr ( Larabci: فاطمة بنت المنذر بن الزبير‎ ) (668-763) malamar hadisi ce daga madina, wanda ta kasance daga zuriyar tabi'un .

Fatima bint Mundhir
Rayuwa
Haihuwa 7 century
Ƴan uwa
Mahaifi Q16119564
Abokiyar zama Hisham ibn Urwah (en) Fassara
Sana'a
Sana'a muhaddith (en) Fassara da Islamicist (en) Fassara

Fatima bint Mundhir ta sami iliminta akan hadisai daga Asma bint Abubakar da Ummu Salamah .A matsayin hujjar isar da ilimi daga gare su a cikin jerin masu watsawa a cikin tarin hadisai shida, sunan Fatima bint Mundhir ta mamaye matsayi na biyu.

Gudunmawa ga manyan tarin hadisai shida

gyara sashe

hadisai guda 21 a cikin sahihul Bukhari da aka ambaci sunanta,a cikin biyu kai tsaye:a hadisi na 922,a cikin littafi na 11,da hadisi na 5783,a cikin littafi na 76.[1]

A cikin Sahihu Muslim akwai hadisai guda 9,inda a hadisi na 5740 a cikin littafin 39 Fatima bint Muhdhir ta zo tare da diyarta Urwa bint Zubair.[2]

A cikin littafin Sunan Abu Dawud akwai hadisai 5,a cikin Jami'at-Tirmizi akwai hadisai 3, adadinsu daya a cikin Sunnan al-Sughra, a Sunan Ibn Majah kuma hadisai 4 ne.

Fatima bint Mundhir ta auri dan uwanta Hisham bn Urwah bn al-Zubayr,wanda ya kasance mashahurin malami a hadisai kuma ya haddace hadisai da dama daga wajen antinsa Aisha.[3] Wani abin sha'awa shi ne,ta haddace mafi yawan hadisai fiye da mijinta, saboda koyi da Asmau bint Abubakar. Duk da kasancewarta malamar hadisi,ta zama daya daga cikin manya-manyan wakilan mata na tsararrakin tabi'un,ta samu matsayin faqihi (fakihu).

  1. http://qaalarasulallah.com/hadith[permanent dead link].
  2. http://qaalarasulallah.com/hadith[permanent dead link].
  3. Waddy, C. (1980). Women in Muslim History. Longmann: University of Virginia, p.72.