Fallou Njie (an haife shi a ranar 5 ga watan Janairu 1999) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Gambiya.

Fallou Njie
Rayuwa
Haihuwa Banjul, 5 ga Janairu, 1999 (25 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob gyara sashe

Ya fara babban aikinsa na wasan kwallon kafa a Italiya a ranar 7 ga Disamba 2017, ya sanya hannu kulob din Seria D Chieri.[1]

A lokacin rani na shekarar 2018, ya sanya hannu tare da kulob din Seria A Genoa kuma an ba da shi ranceny zuwa ga kulob ɗin Arezzo a Serie C. Ya koma Genoa a watan Janairun 2019 ba tare da ya buga wa Arezzo wasa ba kuma ya taka leda a kungiyar Genoa ta Under-19 na sauran kakar wasan.

A ranar 9 ga watan Agusta 2019, ya koma wani kulob na Seria C Avellino a kan aro na tsawon kakar wasa. [2] Ya buga wasansa na farko na ƙwararre a Seria C a kulob ɗin Avellino a ranar 6 ga watan Oktoba 2019 a wasan da suka yi da Rende. Ya fara wasan kuma aka sauya shi a hutun rabin lokaci.[3]

Manazarta gyara sashe

  1. "DUE MOVIMENTI IN CASA DEGLI AZZURRI, ARRIVA NJIE E SALUTA BECCHIO" (Press release) (in Italian). Chieri . 7 December 2017.
  2. "INGAGGIATI I GIOVANI DIFENSORI NJIE E PETRUCCI" (Press release) (in Italian). Avellino. 9 August 2019.
  3. "Avellino v Rende game report" . Soccerway. 6 October 2019.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe