Fathu Abdullahi Mani (haihuwa 1942) a Malumfashi, Jihar Katsina. Fathu yayi aiki a bankin First Bank (Nijeriya), sannan a matsayin kwamishina na ma’aikatar tattalin arziki da ci gaba sannan kuma kwamishinan watsa labarai, harkokin gida sa kuma NIPPSS. Ya rike matsayin chiyaman na Bankin HCB. Fathu ya kirkiri Beto Ginning Company Limited a 2000 a Malumfashi, a matsayin chiyaman na kamfanin.[1][2]

Farkon rayuwa da Ilimi

gyara sashe

An haifi Fathu Abdullahi Mni a 1942 a Malumfashi, Jihar Katsina. ya fara karatun sa ne a Malumfashi inda daga bisani ya kom a makarantar Katsina Middle School da kuma Katsina Teachers College. Ya samu shaidar diploma a harkokin jama’a daga London College.

Fathu ya fara aikin koyarwa daga baya kuma ya koma aikin banki a First Bank Nig Plc. Daga baya yaje London inda yayi aiki da BBC, inda yayi karatun diploma daga kwalejin London a fannin harkokin jama’a. Fathu ya dawo gida Najeriya a 1973, inda yayi aiki da gwamnatin tsakiyar Najeriya da ke Kaduna. Fathu yayi aiki a bankin First Bank Plc, sannan a matsayin kwamishina na ma’aikatar tattalin arziki da ci gaba sannan kuma kwamishinan watsa labarai, harkokin gida sa kuma NIPPSS. Ya rike matsayin chiyaman na Bankin HCB. Fathu ya kirkiri Beto Ginning Company Limited a 2000 a Malumfashi, a matsayin chiyaman na kamfanin.

Fathu ya rasu a ranar Lahadi, 11 March, 2012.

Manazarta

gyara sashe
  1. Alessandro, Del Sole, (2010). Visual Basic 2010 unleashed. Sams Pub. ISBN 978-0-672-33100-8. OCLC 874922564.
  2. https://www.reuters.com/markets/companies/UNTL.LG. Retrieved 2022-05-27.