Fahardine Hassani (an haife shi ranar 7 ga watan Nuwamba 1993) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Comoriya wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Comoros.[1]

Fahardine Hassani
Rayuwa
Haihuwa Faransa, 7 Nuwamba, 1993 (31 shekaru)
ƙasa Komoros
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Football Bourg-en-Bresse Péronnas 01 (en) Fassara2013-2015
Sporting Club Lyon (en) Fassara2016-2017
FC Bourgoin-Jallieu (en) Fassara2017-2020
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga

Hassani ya kwashe gaba dayan kuruciyarsa yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Olympque de Vaulx, kuma ya koma kulob ɗin Football Bourg-en-Bresse Péronnas 01 a matsayin mai tsaron gida.[2] Bayan nasarar halarta ta farko tare da kungiyar kwallon kafa ta CS Bourgoin-Jallieu a cikin shekarar 2017, Hassani ya sami kira zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Comoros.[3]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Hassani ya fara buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Comoros da rashin nasara da ci 3-0 a gasar cin kofin COSAFA na shekarar 2018 da ƙasar Mozambique a ranar 29 ga watan Mayu 2018.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Fahardine Hassani at Soccerway
  2. "Actualité - FAHARDINE HASSANI, UN GARDIEN PROMETTEUR - club Football Lyon Duchère A.S. - Footeo" . duchere.footeo.com .
  3. "Foot : Le berjallien Fahardine Hassani sélectionné avec les Comores - LSD - Le Sport Dauphinois" . 9 November 2017.
  4. "Mozambique - Comores : Cosafa Cup 2018" .