Eric Aghimien
Eric Enomamien Aghimien darekta ne na Najeriya, furodusa, marubucin allo kuma edita. [1]Fim ɗin sa na farko, A Mile daga Gida ya sami lambobin yabo a duka 2014 Africa Magic Viewers Choice Awards da lambar yabo ta 10th Africa Movie Academy Awards.[2]
Eric Aghimien | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Birnin Kazaure, 21 ga Janairu, 1982 (42 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Auchi Polytechnic (en) |
Sana'a | |
Sana'a | marubin wasannin kwaykwayo, darakta, editan fim da mai tsara fim |
Muhimman ayyuka | A Mile from Home |
IMDb | nm6325921 |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Eric Aghimien a birnin Benin na jihar Edo kuma shi ne na hudu a cikin yara bakwai. Yana dan shekara takwas yana makarantar firamare ya fara zanen ban dariya da kuma sayar wa abokan karatunsa [3]. Ya halarci Kwalejin Immaculate Conception, Benin City da Auchi Polytechnic, Jihar Edo, Nigeria. Eric a dabi'ance yana da hazaka da fasahar kere kere wanda ya hada da; waƙa, gyare-gyare da zane. Babban abin sha'awar sa tun yana yaro shine; kallon fina-finai banda wasan ninkaya da kwallon kafa.[4]
Ya samu Diploma na kasa a fannin fasahar dakin gwaje-gwaje na Kimiyya a shekarar 2005 [5]. Yayin da yake samun difloma, ya kasance memba na ƙungiyar kiɗa da ake kira Da TED [6]. Bayan Diploma na Kasa, Eric ya yanke shawarar yin aiki a cikin nishaɗi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Awoyinfa, Samuel (July 17, 2013). "Forgiveness Is Key In 'A Mile From Home'". Punch. Archived from the original on 2014-05-12.
- ↑ Akinseye, Isabella. ""I was detained for nine days by Customs for importing props…" Eric Aghimien". nollysilverscreen.com/. Retrieved 19 August 2014.
- ↑ Agbedeh, Terh. "I made A Mile from Home with very little expectation – Eric Aghimien". www.thenicheng,com. Retrieved 8 April 2015.
- ↑ Williams, Yvonne. "'I worked as a waiter in some restaurants '– Eric Aghimien, Director, A Mile from Home". happenings.com.ng. Retrieved 8 April 2015.
- ↑ Williams, Yvonne. "'I worked as a waiter in some restaurants '– Eric Aghimien, Director, A Mile from Home". happenings.com.ng. Retrieved 8 April 2015.
- ↑ Nwelue, Onyeka. "A MILE FROM HOME IS A GREAT FILM by Onyeka Nwelue". www.sabinews.com. Retrieved 8 April 2015.