Elman Peace and Human Rights Center
Cibiyar Zaman Lafiya da 'Yancin Dan Adam ta Elman. Kungiya ce mai zaman kanta da ke zaune a Mogadishu, a kasar Somaliya . Fartuun Adan ce ta kafa ta don girmama marigayi mijinta Elman Ali Ahmed, ɗan kasuwa na gida kuma mai fafutukar zaman lafiya. An kafa kungiyar ne a cikin shekarar dubu daya da dari tara da casa'in (1990), kuma an sadaukar da ita don inganta zaman lafiya, haɓaka jagoranci da kuma karfafa wa 'yan majalisa da aka ware su zama masu yanke shawara a cikin hanyoyin da ke tabbatar da jin daɗinsu.
Elman Peace and Human Rights Center | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Shirin farko na kasar don taimakawa wadanda ke fama da tashin hankali na jinsi, yana ba da shawara, kiwon lafiya da Kuma tallafin gidaje ga mata masu bukata. Ayyukan Elman sun taimaka wajen wayar da kan jama'a a cikin gida game da batun, kuma sun karfafa canje-canje a cikin manufofin gwamnati. Ilwad ya kuma gudanar da bita na ilimi ta hanyar cibiyar ga masu rauni a cikin al'umma, kuma ya tsara da aiwatar da ayyukan da ke inganta wasu damar rayuwa ga matasa da tsofaffi.