Elisabeth Tankeu (29 Fabrairu 1944 – 16 Oktoba 2011) 'yar siyasar Kamaru ce. Ita ce kwamishiniyar ciniki da masana'antu ta Tarayyar Afirka.[1]

Elisabeth Tankeu
Rayuwa
Haihuwa Yabassi (en) Fassara, 29 ga Faburairu, 1944
ƙasa Kameru
Mutuwa Neuilly-sur-Seine (en) Fassara, 16 Oktoba 2011
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Aiki siyasa gyara sashe

Daga shekarun 1976 zuwa 1979 Tankeu ta kasance mataimakiyar darakta mai kula da tsare-tsare na Kamaru sannan daga shekarun 1980 zuwa 1983 ta kasance Darakta a wannan ma'aikatar. Daga shekarun 1983 zuwa 1988 ta kasance mataimakiyar ministar tsare-tsare ta masana'antu sannan daga shekarun 1988 zuwa 1992 ministar tsare-tsare da raya yankuna.[2]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Tankeu ta mutu a ranar 16 ga watan Oktoba 2011 a wani asibiti a Paris, Faransa.[3] An binne ta ne a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2011 a Bangoua, garin mahaifar mijinta a yammacin Kamaru.

Manazarta gyara sashe

  1. "Countries in Africa plan tack for G-8 meeting". The New York Times. 5 July 2005. Retrieved 2009-10-20.
  2. "Countries in Africa plan tack for G-8 meeting". The New York Times. 5 July 2005. Retrieved 2009-10-20.
  3. "Cameroon mourns: Former Minister Elisabeth Tankeu dies in Paris". Cameroon Radio & Television. 18 October 2011. Archived from the original on 17 January 2012. Retrieved 20 October 2011.