Egbu
Egbu wani kauye ne a karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar Imo a kudancin Najeriya, wanda ke dai-dai kogin Otamiri kusa da birnin Owerri. Egbu na daga cikin ‘yan uwa a garin owerri da ake kira “Ala Enyi” da suka haɗa da; Ihitta Ogada, Awaka, Owerri Nchi Ise and Naze. Garin Egbu na da alaƙa da wasu garuruwa da ƙauyuka ta hanyar Owerri – Umuahia.
Egbu | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Yawan mutane | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Ƙauyuka
gyara sasheƘauyen Egbu ya ƙunshi ƙananan ƙauyuka biyar: Umuofor, Mpama, Umuayalu, Ofeuzo da Ishiuzo. Egbu ya yi iyaka da Owerri, Awaka da Naze. Garin yana kusa da babban birnin Owerri. Egbu na ƙarƙashin jagorancin EZE Ochoroma ta Egbu, shugaban gargajiya ɗaya tilo a cikin al’umma. Egbu shine tushen farko a zahiri na kogin Otamiri wanda ke gudana zuwa Owerri Nchi Ise, Nekede, Ihiagwa sannan ya ratsa ta wasu al'ummomi da yawa a cikin jihar IMO zuwa jihar Rivers. A cikin 1906 zuwa 1912, Egbu shine inda Thomas Dennis na ƙungiyar Mishan na Church da abokan aikinsa, ƙarƙashin CMS yanzu Anglican Church suka fassara Littafi Mai Tsarki na Ibo na farko. A halin yanzu All Saints Cathedral Egbu.