Ebenezer Andrews

ɗan wasan badminton ɗan Ghana

Ebenezer Andrews (21 Mayu 2000) ɗan wasan badminton ɗan Ghana ne.[1] A watan Afrilun 2019, yana cikin tawagar Ghana da ta ci tagulla a Gasar Wasannin Mixed Team Championship da aka gudanar a Port Harcourt, Nigeria.[2]

Ebenezer Andrews
Rayuwa
Haihuwa Winneba (en) Fassara, 21 Mayu 2000 (24 shekaru)
ƙasa Ghana
Harshen uwa Turanci
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Mai wasan badminton

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Andrews ya fito daga Winneba a yankin Tsakiyar Ghana.[3][4] Shi dalibi ne na Jami'ar Ilimi, Winneba.[5]

Andrews ya halarci gasar Badminton na matasa na 2013 (U-19) da aka gudanar a Aljeriya.[6]

Ya kuma halarci gasar wasannin Afirka karo na 10 a jami'ar Kenyatta dake birnin Nairobin kasar Kenya.[5]

Nasarorin da aka samu

gyara sashe

Andrews da Eyram Migbodzi guda biyu sun doke takwarorinsu na Ivory Coast Doulo Lou Annick da Ousmane Ovedroogo da ci 21-12 da 21-13 inda suka yi nasara a gasar ta maza.[2]

A gasar Commonwealth ta 2018 da aka gudanar a Ostiraliya, Andrews da biyunsa Daniel Doe sun ci zinare a 2-1 cikin uku da suka yi da Emmanuel Botwe da Abraham Ayittey a wasan karshe na biyu.[7]

A watan Maris na 2022, kungiyar Badminton ta Ghana ta dakatar da Andrews da sauran 'yan wasan Badminton kuma an tabbatar da cewa ba su cancanta ba.[8]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Ebenezer Andrews live scores, results, fixtures | Flashscore.com / Badminton". www.flashscore.com (in Turanci). Retrieved 2023-03-01.
  2. 2.0 2.1 llc, Online media Ghana. "Ghana wins bronze at 2019 All Africa Badminton Mixed Team Champs :: Ghana Olympic Committee". ghanaolympic.org (in Turanci). Archived from the original on 2023-03-01. Retrieved 2023-03-01.
  3. Afful, Henrietta (2022-03-15). "Ghana Badminton cracks whip: Expels 6, suspends 4". GBC Ghana Online - The Nation's Broadcaster | Breaking News from Ghana, Business, Sports, Entertainment, Fashion and Video News (in Turanci). Retrieved 2023-03-01.
  4. GNA. "BAG prepares for Africa Games Qualifiers | News Ghana". https://newsghana.com.gh (in Turanci). Retrieved 2023-03-01. External link in |website= (help)
  5. 5.0 5.1 "University of Education to Compete in 10th FASU Games in Kenya - Athleticshour.com" (in Turanci). 2022-06-05. Retrieved 2023-03-01.[permanent dead link]
  6. "Ghana to compete in Africa Badminton Junior Championships - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2013-03-15. Retrieved 2023-03-01.
  7. "Ghana Badminton team sweeps victory at Under 19 Championship". The Ghana Guardian News (in Turanci). Retrieved 2023-03-01.
  8. "Badminton: BAG cracks whip on officials, players". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2023-03-01.