Dylan Budge
Dylan Evers Budge (an haife shi ranar 11 ga watan Satumba, 1995). Dan wasan kurket ne na kasar Scotland ne. Ya buga wasansa na farko na One Day International (ODI) don Scotland da Ingila a ranar 10 ga Yunin 2018. Ya buga wasansa na Twenty20 International (T20I) na farko don Scotland da Pakistan a ranar 12 ga Yunin 2018.
Dylan Budge | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Leeds, 11 Satumba 1995 (29 shekaru) |
ƙasa | Birtaniya |
Karatu | |
Makaranta | Woodhouse Grove School (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | cricketer (en) |
Wasan kurket
gyara sasheA cikin watan Yunin 2019, an zaɓe shi don wakiltar Scotland A a cikin rangadin da suka yi zuwa Ireland don buga Ireland Wolves A cikin Yuli 2019, an zaɓi shi don buga wa Edinburgh Rocks a bugu na farko na gasar kurket ta Euro T20 Slam. Sai dai a wata mai zuwa aka soke gasar.
A cikin Oktoba 2019, an ƙara shi cikin tawagar Scotland gabanin wasannin share fage a gasar share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2019 ICC T20 a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya maye gurbin Ollie Hairs, wanda aka cire shi saboda rauni. A cikin Satumba 2021, an sanya sunan Budge a cikin tawagar wucin gadi ta Scotland don Gasar Cin Kofin Duniya na maza na T20 na 2021 ICC .
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Dylan Budge at ESPNcricinfo
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |