Dolton, Devon
Dolton ƙaramin ƙauye ne da Ikklesiya ta farar hula a cikin gundumar Torridge na Devon, dake a kudu maso yammacin Ingila, kewaye, daga arewa, ta Beaford, Ashreigney, Winkleigh, Dowland, Meeth, Huish da Merton.[1] Ƙauyen na da yawan jama'a kusan 900.[2]
Dolton, Devon | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Birtaniya | |||
Constituent country of the United Kingdom (en) | Ingila | |||
Region of England (en) | South West England (en) | |||
Ceremonial county of England (en) | Devon (en) | |||
Non-metropolitan county (en) | Devon (en) | |||
Non-metropolitan district (en) | Torridge (en) | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 838 (2021) |
An ambaci Dolton a cikin Littafin Domesday na 1086 a matsayin Duueltone. Sunan na iya nufin "gidan gona a cikin buɗaɗɗen ƙasar da kurciya ke yawan zuwa" ( Old English dūfe + feld + tunun ).[3]
Hanyar Tarka ta wuce ta Dolton. An sadaukar da cocin Ikklesiya ga St Edmund. Gidan tarihi na Stafford Barton yana kusa da shi. Dolton tagwaye ne tare da Amfreville a Faransa, da Hillerse a Jamus.
Anthony Horneck FRS, masanin tauhidin Furotesta, ya zauna a Dolton tsakanin 1670 da 1671.[4] Henry Bentinck, 11th Earl na Portland, ya zauna a wani gida mai suna Little Cudworthy kuma ya mutu a can a shekarar 1997. Mawaƙin Rolling Stones drummer Charlie Watts ya rayu a Halsdon House kusa da ƙauyen na wasu shekaru har izuwa mutuwarsa a shekaran 2021.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Map of Devon Parishes" (PDF). Devon County Council. Archived from the original (PDF) on 2 November 2013. Retrieved 7 July 2016.
- ↑ "Three Bridges Ward 2011". Archived from the original on 16 February 2015. Retrieved 16 February 2015.
- ↑ Hanks, Patrick; Hodges, Flavia; Mills, A. D.; Room, Adrian (2002). The Oxford Names Companion. Oxford: the University Press. p. 1011. ISBN 978-0-19-860561-4.
- ↑ "Horneck, Anthony". Cambridge University. Archived from the original on 2013-04-19.
- ↑ Paul Donovan (25 August 2011). "Villagers get a rare chance to meet rock star neighbour". North Devon Journal. Archived from the original on 3 December 2013. Retrieved 11 March 2013.