Dennis Nnamdi Agbo
Dennis Nnamdi Agbo (an haife shi a ranar 15 ga watan Maris 1964) ɗan siyasan Najeriya ne. A yanzu haka ya zama ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazaɓar Igbo-Eze ta Arewa/Udenu na jihar Enugu a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10. [1] [2]
Sana'a
gyara sasheA shekarar 2024, Dennis Nnamdi Agbo na jam’iyyar Labour Party (LP) ya samu nasarar lashe kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Igbo-eze North/Udenu bayan da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta soke nasarar da Simon Atigwe ya samu. Atigwe na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaɓen da aka yi a watan Fabrairun 2024, amma Agbo ya ƙalubalanci sakamakon. [3] [4]
A ranar 14 ga watan Agusta ne kotun ta yanke hukunci kan goyon bayan Agbo, inda ta soke kuri’u 2,000 na Atigwe tare da tabbatar da Agbo a matsayin wanda ya yi nasara na gaskiya bisa sakamakon zaɓen shekarar 2023. [5] [6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Odunewu, Olusegun (2024-10-09). "Appeal Court reinstates LP's Dennis Agbo, sacks PDP's Simon Atigwe in Enugu". National Daily Newspaper (in Turanci). Retrieved 2024-12-24.
- ↑ "Dennis Agbo: l'm Fulfilled Giving my People Quality Representation – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2024-12-24.
- ↑ Bankole, Idowu (2024-10-09). "Appeal Court sacks Enugu PDP Rep, returns Agbo of Labour Party". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-24.
- ↑ Ugwu, Francis (2024-08-14). "Tribunal sacks Enugu Rep member, declares LP candidate winner". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-24.
- ↑ sunnews (2024-08-16). "Labour Party reclaims National Assembly seat". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-24.
- ↑ Ede, Raphael (2024-02-04). "Enugu rerun: PDP wins federal constituency seat". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-24.