Dawn of a New Day (fim)
Dawn of a New Day ( Egyptian Arabic , Fagr Yom gedid ) fim ne na Masar a shekara ta 1965 wanda Youssef Chahine ya ba da Umarni.[1][2][3] Samir Nasri da Abd al-Rahman Sharqawi ne suka rubuta, Sanaa Gamil, na cikin jaruman shirin.
Dawn of a New Day (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1965 |
Ƙasar asali | Misra |
Characteristics | |
Direction and screenplay | |
Darekta | Youssef Chahine (en) |
'yan wasa | |
External links | |
Specialized websites
|
Shirin fim ɗin ya biyo bayan wani labari mai ban tausayi na soyayya wanda ta hanyarsa ne aka haska haske game da damuwar da ajin Burgeois suka sha bayan juyin juya halin Masar a shekara ta 1952, yayin da wannan ajin ya kasa shawo kan sabbin canje-canje a cikin al'umma. Darakta Chahine ta bayyana damuwar bourgeoisie bayan juyin juya hali ta hanyar wata mata da ke neman kanta ba tare da jinkiri ba a cikin sabuwar duniya da ba ta saba da ita ba.[4][5][6]
Sharhi
gyara sasheNayla, mai shekaru 40, matar wani hamshakin attajirin ne, wanda ya aure ta a matsayin matashiya mai kayatarwa kuma ya mayar da rayuwar ta cikin ƙunci. Ta yi ƙoƙarin yin haɗin gwiwa da duniyar da ta saba sani. Ta haɗu da wani matashi mai suna Tariq, kuma tana sha'awar saukinsa. Bata zabar wani namiji a ajin ta, musamman Abu Al-Ela da yake ƙoƙarin kusantarta. idan ta matso kusa da Tariq da duniyarsa sai tunanin abubuwan da suka faru a baya ya mamaye ta, sai aka shiga tattaunawa mai tsanani a tsakanin su, inda ta bayyana cewa kowannen su ya kasa mu’amala da daya, don haka ta yanke shawara a karshe. nisantarsa.
Yan wasan shirin
gyara sashe- Sanaa Gamil a matsayin Nayla
- Saif Abdelrahman a matsayin Tariq
- Hamdy Gheith a matsayin Hussein Abu El-Ela
- Soher El Bably a matsayin Huda
- Madiha Salem a matsayin Samira
- Youssef Chahine a matsayin Hamada
- Hassan El Baroudy a matsayin Hassan
- Abdel Khalek Saleh a matsayin Abddallah
- Badr Noufal
- Mohammed Yeh
- Laila Yousry
- Fattouh Nashaty
Manazarta
gyara sashe- ↑ Fawal, Ibrahim (2019-07-25). Youssef Chahine (in Turanci). Bloomsbury Publishing. ISBN 978-1-83902-134-3.
- ↑ Vitali, Valentina; Willemen, Paul (2019-07-25). Theorising National Cinema (in Turanci). Bloomsbury Publishing. ISBN 978-1-83902-084-1.
- ↑ Russell, Sharon A. (1998-02-18). Guide to African Cinema (in Turanci). Bloomsbury Publishing USA. ISBN 978-1-56750-911-3.
- ↑ Fagr Yom gedid | Film | 1964 (in Harshen Polan), retrieved 2023-10-25
- ↑ "Single Media | MIF Site". Retrieved 2023-10-25.
- ↑ Hopkins, Harry (1969). Egypt, the Crucible: The Unfinished Revolution in the Arab World (in Turanci). Houghton Mifflin. ISBN 978-0-436-20151-6.