Davy Van Den Berg
Dave Johannes Andreas van den Berg (an haife shi ranar 4 ga watan Fabrairu, 2000) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Netherlands wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar PEC Zwolle na league din Eredivisie.[1]
Davy Van Den Berg | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Dave Johannes Andreas van den Berg | ||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Uden (en) , 4 ga Faburairu, 2000 (24 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Kingdom of the Netherlands (en) | ||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Dutch (en) | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna | Dutch (en) | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya |
Shekarun farko
gyara sasheVan den Berg ya buga wasan kwallon kafa na matasa a kungiyar UDI '19, kafin ya shiga makarantar koyon kwallon matasa ta PSV Eindhoven a 2008.[2]
A ranar 3 ga watan Oktoban 2018, Van den Berg ya kasance cikin kungiyar PSV ta U-19 da ke fafatawa a UEFA Youth League, karkashin babban koci Ruud van Nistelrooy. Ya fara buga wasansa na farko a gasar da Inter Milan ta ‘yan kasa da shekara 19, inda ya zo a matsayin dan chanji a madadin Rico Zeegers a ci 2-1. A ƙarshen 2018, Van den Berg ya samu sabani da kocinsa Van Nistelrooy ba, kuma an dakatar da kwangilarsa ta hanyar amincewar juna.[3]
Ya shiga addinin Musulunci kuma yana burge mutane a kafafen sada zumunta tare da karatun Alqur'ani mai Girma, musamman inda matashin dan shekara 22 yana karanta ayoyi daga Suratul Nazi’at.[4]
Utrecht
gyara sasheVan den Berg ya koma FC Utrecht a ranar 13 ga watan Fabrairun 2019 akan canja wuri kyauta, watau free transfer kenan inda ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa 2021 tare da zaɓi na ƙarin shekara.[5] Ya fara buga wasansa na farko ga kungiyar rejin Jong FC Utrecht, inda ya fafata a matakin na biyu na Eerste Divisie, a ranar 18 ga watan Oktoban 2019 a wasan da suka tashi 2-2 gida da De Graafschap, wanda ya shigo a madadin dan chanji ga dan wasannan Hicham Acheffay.
A ranar 9 ga Satumba 2020, an tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2023 gami da zaɓi na ƙarin shekara.[6]
Ya buga wasansa na farko na Eredivisie a Utrecht a ranar 29 ga watan Agustan 2021 a matsayin dan chanji a wasan da suka yi da kungiyar Feyenoord.
A ranar 31 ga watan Janairun 2022, an ba da aron van den Berg zuwa kungiyar Roda JC Kerkrade.
PEC Zwolle
gyara sasheVan den Berg ya shiga kungiyar PEC Zwolle a ranar 4 ga watan Agustan 2022, inda ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyu tare da zaɓi na ƙarin shekara. Ya buga wasansa na farko a kulob din a ranar 7 ga watan Agusta, inda ya fito daga benci don maye gurbin Tomislav Mrkonjić a rabin lokacin gasar lig da ta doke De Graafschap da ci 2-1.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.vi.nl/spelers/davy-van-den-berg/profiel
- ↑ https://www.ed.nl/psv/fc-utrecht-neemt-davy-van-den-berg-19-definitief-over-van-psv~ac910b17/
- ↑ https://www.rodajckerkrade.nl/nieuwsbericht/31-03-2022/davy-gunt-de-roda-jc-fans-promotie-van-harte
- ↑ https://islamchannel.tv/blog-posts/video-watch-dutch-muslim-convert-footballer-davy-van-den-berg-recites-the-quran
- ↑ https://utrecht.nieuws.nl/sport/70727/davy-van-den-berg-sluit-aan-bij-jong-fc-utrecht/
- ↑ https://www.fcupdate.nl/voetbalnieuws/339432/psv-onder-19-wordt-beloond-en-wint-laat-van-inter/