David Ajang
David Ajang (an haife shi a cikin shekara ta alif ɗari tara da saba'in 1970 A.C)a ƙaramar hukumar Zariya ɗan Najeriya ne mabiyin Cocin Katolika wanda ke aiki a matsayin bishop na Diocese Roman Katolika na Lafia.[1] An naɗa shi bishop a shekarar 2021.[2]
David Ajang | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Suna | Dauda |
Shekarun haihuwa | 31 ga Maris, 1970 |
Wurin haihuwa | Zariya |
Sana'a | Catholic priest (en) da Catholic bishop (en) |
Muƙamin da ya riƙe | diocesan bishop (en) |
Addini | Cocin katolika |
Consecrator (en) | Antonio Filipazzi (en) , Ignatius Ayau Kaigama (en) da Matthew Ishaya Audu (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haife shi a shekara ta 1970, daga shekarar 1982 David Ajang ya halarci makarantar sakandare ta Saint John Vianney Minor Seminary a Barkin Ladi, kuma daga shekarar 1987 zuwa 1990 ya karanta falsafa a Saint Thomas Aquinas Major Seminary a Makurɗi kuma daga shekarar 1990 zuwa 1994 tauhidin Katolika a Saint Augustine's Major Seminary a Major. A ranar 3 ga watan Disamban 1994, aka naɗa shi firist.
A shekarun baya-bayan nan, ya kasance limamin gwamnan jihar Filato tun a shekara ta 2015 da kuma limamin cocin Immaculate Conception parish kuma shugaban jami’ar Zaramaganda tun daga shekara ta 2018.
A ranar 31 ga watan Maris ɗin 2021, Paparoma Francis ya naɗa shi Bishop na Lafia. An naɗa shi bishop ne a ranar 24 ga watan Yuni a St. William's Cathedral a jihar Lafia nassarawa.