Dashnor Kokonozi
Dashnor Kononozi (an haife shi 21 ga Yuni 1951) ɗan jarida ne kuma marubuci ɗan ƙasar Albaniya wanda ya kafa Cibiyar Kayayyakin Al'adu ta ƙasa (NCCPI) kuma shine darekta na farko.
Dashnor Kokonozi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tirana, 21 ga Yuni, 1951 (73 shekaru) |
ƙasa | Albaniya |
Karatu | |
Harsuna | Albanian (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida da marubuci |
Gadon Al'ada
gyara sasheKokonozi ya kafa hukumar NCCPI a farkon shekarun 1990 bayan tabarbarewar doka da oda a Albaniya bayan hambarar da gwamnatin gurguzu ta kai ga wawure kayayyakin tarihi na al'adu. Bukatun da Interpol ta yi na neman taimako wajen gano abubuwan da aka wawashe, ya nuna cewa akwai karancin bayanai a Albaniya kuma Kokonozi ya shawo kan Bankin Duniya da ya ba da kudin samar da kayyaki na farko na kasa.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Albania Struggles to Catalogue its Unknown Treasures. BalkanInsight, 30 October 2010. Retrieved 10 November 2015.