Colette Samoya Kirura
Colette Samoya Kirura (an haife ta a shekara ta 1952) tsohuwar 'yar siyasa ce kuma jami'iyyar diflomasiyya. A shekarar 1982 ta zama ɗaya daga cikin rukunin mata na farko a majalisar dokokin ƙasar. Bayan shekaru goma, an naɗa ta a matsayin wakiliyar dindindin ta ƙasar a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Colette Samoya Kirura | |||||
---|---|---|---|---|---|
1992 - 1994
1982 - 1987 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 1952 (71/72 shekaru) | ||||
ƙasa | Burundi | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya, gwagwarmaya da marubuci | ||||
Mamba | Parliament of Burundi (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Samoya Kirura a Nyakirwa a shekara ta 1952. [1] Ita ce yarinya ta farko daga ƙauyensu da ta shiga makarantar sakandare kuma ta ci gaba da zama ɗaya daga cikin matan Burundi na farko da suka sami digiri na biyu, inda ta kammala karatu a fannin ƙasa da tarihi. [2] Daga baya ta yi aiki a matsayin farfesa a jami'a. [2]
Ta kasance 'yar takara a zaɓen 'yan majalisa na shekarar 1982 kuma an zaɓe ta a Majalisar Dokoki ta ƙasa, ta zama ɗaya daga cikin rukuni na farko na 'yan majalisa. [2] Ta ci gaba da zama a Majalisar Dokoki ta ƙasa har zuwa juyin mulkin 1987, bayan haka ta zama shugabar kungiyar matan Burundi, matsayin da ta riƙe har zuwa shekara ta 1991. [2]
A shekarar 1992 aka naɗa Samoya Kirura a matsayin wakiliya ta dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva, mace ta farko da ta wakilci Burundi. [1] Bayan barin muƙamin a shekarar 1994, ta kafa kungiyar zaman lafiya ta "Bangwe et dialogue" a cikin shekarar 1998. [2] Daga baya ta zauna a Geneva kuma ta zama mai ba da shawara ga ayyukan NGO. [1] A cikin shekarar 2002 ta buga wani littafi La femme au regard triste ( Matar da ke da idanu masu bakin ciki ). [1]