Cibiyar Sinai
Cibiyar Sinai Kungiya ce mara riba mai zaman kanta wacce aka kirkira a shekarar 1998 don haskakawa da adana al'adu da tarihin yankin Sinai. Cibiyar ta kasance a Kudancin Sinai, Masar, kuma tana da niyyar kiyaye rayuwar Badawiyya, don kada al'adun su bace kamar sauran al'adu a baya. Cibiyar Sinai tana da ƙaramin ɗakin karatu kuma tana baje kolin abubuwa na al'adun Badawiyya kamar kayan ado, tufafi, kayan aiki, da makamai.
Cibiyar Sinai | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata, nonprofit organization (en) da non-governmental organization (en) |
Mulki | |
Hedkwata | Dahab (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1998 |
centre4sinai.com.eg |
Cibiyar tana ba da balaguro zuwa cikin hamada ta raƙumi ko keken dutse. Haka kuma kungiyar ta himmatu wajen tsaftace yankin Sinai da kuma kiyaye ta a haka.
Manazarta
gyara sashe- Centre for Sinai Archived 2019-04-23 at the Wayback Machine