Chiroma Mashio ɗan siyasan Najeriya ne. Shi ne shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe a yanzu. Yana wakiltar mazaɓar Jajere kuma an zaɓe shi ba tare da hamayya ba a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe ta 8. [1] [2]

Chiroma Mashio
Rayuwa
Sana'a

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Chiroma a ranar 25 ga watan Mayu, 1968, a garin Mashio, dake cikin ƙaramar hukumar Fune a jihar Yobe. Ya fara karatun sa na farko a makarantar firamare ta Mashio kafin ya halarci makarantar sakandiren gwamnati da ke Damagum. Don neman karin ilimi, ya halarci Ramat Polytechnic da ke Maiduguri, daga nan kuma ya wuce Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digirin farko na Kimiyya (B.Sc.) a Kimiyyar Siyasa. [3]

Aikin siyasa

gyara sashe

Chiroma ya ci gaba da tafiyar siyasa a lokacin da aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokokin jihar Yobe, mai wakiltar mazaɓar Jajere a shekarar 1999. [4] A tsawon shekaru, ya yi aiki a cikin kwamitoci daban-daban da kuma matsayin jagoranci a cikin zauren majalisa. Musamman ma shi ne shugaban kwamitin Kuɗi da kasafin kuɗi na majalisar a lokacin majalissar ta 7. [5]

A majalisa ta 8, 'yan uwansa 'yan majalisar ne suka zaɓe shi baki ɗaya. [5] [6]

Manazarta

gyara sashe
  1. Hemba, Joe (2023-06-26). "Yobe State House of Assembly inaugurated, new speaker elected". www.premiumtimesng.com. Archived from the original on 2025-01-03. Retrieved 2025-01-03.
  2. "8th Assembly Yobe State House Of Assembly 24 Members". Yobe State House of Assembly. 2022-04-07. Archived from the original on 2024-12-16. Retrieved 2025-01-03.
  3. Gimba, Habibu (2023-07-08). "Why no one ever challenged my victory in 24 years – Yobe Speaker - Daily Trust". dailytrust.com (in Turanci). Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2025-01-03.
  4. "Why no one ever challenged my victory in 24 years – Yobe Speaker - Daily Trust". dailytrust.com/ (in Turanci). 2023-07-08. Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2025-01-03.
  5. 5.0 5.1 Mingyi, Musa (2023-06-26). "Chiroma-Mashio Emerges Speaker Of Yobe 8th Assembly". Channels Television (in Turanci). Archived from the original on 2023-06-29. Retrieved 2025-01-03. Cite error: Invalid <ref> tag; name "CTV-26J" defined multiple times with different content
  6. Odili, Esther (2023-06-26). "Chiroma Machiyo elected as speaker of 8th Yobe Assembly". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2023-06-27. Retrieved 2025-01-03.