Cecile Esmei Amari (an haife ta a ranar 20 ga watan Nuwamba shekara ta 1991) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta Ivory Coast wacce ke taka leda a matsayin ƴar wasan tsakiya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Ivory Coast . Ta kasance cikin tawagar a Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka ta 2014 da kuma gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2015 . A matakin kulob, tana buga wa Ataşehir Belediyespor wasa mai lamba 7 a Gasar Kwallon Kafa ta Mata ta Turkiyya ta 2019-20 .

Cecile Esmei Amari
Rayuwa
Haihuwa Treichville (en) Fassara, 20 Nuwamba, 1991 (32 shekaru)
ƙasa Ivory Coast
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Kungiyar Kwallon Kafa ta Mata ta Ivory Coast2012-
  Wydad AC2013-
FK Spartak Subotica (en) Fassara2014-2014
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Ta taka leda a Maroko a shekarar 2012 don Raja Haroda Casablanca . A cikin shekara ta 2013, tana tare da Wydad AC a cikin ƙasa ɗaya. An ba ta aro ga ƙungiyar Serbia ZFK Spartak Subotica a cikin shekara ta 2014. [1] [2] [3] [4] [5] [6]

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa na duniya mata na Ivory Coast

Manazarta gyara sashe

  1. "Ivory Coast: Just do not miss". Sportschau. Retrieved 24 April 2017.
  2. "FIFA 2015 World Cup: Group B at a glance". Montreal Gazette. Archived from the original on 25 April 2017. Retrieved 24 April 2017.
  3. "Oyuncular – Futbolcular: Esmei Cecile Amari" (in Harshen Turkiyya). Türkiye Futbol Federasyonu. Retrieved 4 December 2019.
  4. "Côte d'Ivoire – CAN féminine 2012 : La sélection publiée". afrik11.com (in Faransanci). 13 June 2012. Archived from the original on 11 December 2014. Retrieved 4 December 2019.
  5. Gattuso, Raji (13 October 2014). "AWC Namibia 2014: Ivorian Ladies Will Bounce Back- Clementine Toure". Papson Sports. Archived from the original on 8 December 2014. Retrieved 4 December 2019.
  6. "Actualités football féminin". Sporting Féminin Football Club Paris (in Faransanci). Archived from the original on 7 December 2014. Retrieved 4 December 2019.