Camfi hanya ce ta zato da Bahaushe ya gina kansa a kan ta dangane da faruwar wasu abubuwa. Wannan al’ada ta camfi na daga cikin munanan al’adun da Bahaushe ya ke da su tun dauri. Bahaushe yana aƙidantuwa da zance-zance da ya yi dangane da faruwa ko afkuwar wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa. Wannan al’ada masana suna yi mata kallon mummunar al’ada ce. Saboda Kashi tamanin cikin dari duk karyace.

Camfi

Ma’anar Camfi

gyara sashe

A al’adance idan aka ce camfi ana nufin, ƙudurcewa da mutum ya ke yi a zuciyarsa cewa idan ya aikata wani aiki, ko ya faɗi wata magana, ko wani abu ya faru da shi, to sakamakon faruwar wannan abun, wani abu kuma daban, wanda ka iya zama kakkyawa ko akasin haka na iya faruwa da shi. Amma Farfesa Ɗangambo (1984), cewa ya yi, “Camfi, shi ne, mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to, ya gaskata wani abun zai faru, sakamakon haka.”[1]

Su kuwa Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), cewa suka yi, “Wata hanya ce ta ƙudurce aukuwa ko faruwar wani abu da sakamakonsa zai iya zama mai kyau ko mai alheri ko mai muni.” Kenan, bisa la’akari da waɗannan maganganu na masa game da ma’anar camfi, za a iya fahimtar cewa, camfi ƙuduri ne da ake gina shi a kan zato. Saboda, za to ne ake yi cewa idan aka yi wani abu, ko aka faɗi wani abu, da sauran su, to wani abu na iya faruwa. Babu tabbas cikin faruwar wannan abun.[2]

Misalan Camfe-Camfe

gyara sashe

A misalce, Bahaushe ya ƙudurce cewa; 1. Idan mutum ya zauna a ƙofar ɗaki, aljanu suna iya bugunsa.

2. Idan mutum ya ji hannunsa na dama yana ƙaiƙayi, zai samu arziƙi.

3. Idan mutum ya taka kashi da safe, zai samu arziƙi a wannan rana.

4. Idan mutum ya ji ƙafarsa tana ƙaiƙai, to zai yi tafiya.

5 Mutum yaji kukan mujiya,tom za ai rasuwa

Kenan, idan aka lura da waɗannan ƙudurori da suka zo a matsayin misalsalin camfe-camfe, za a fahimci cewa zato ne kawai. Don haka wannan al’ada ba ta da kyau. Kuma masana sun yi gargaɗi da a nesance ta.

Manazarta

gyara sashe
  1. Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.
  2. Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.