Bukukuwan hausawa da rabe-rabensu

A wannan mataki za a yi duba dangane da ma'anar buki daga fahimtar masana da manazarta alkada da kuma zamnatakewar al'umma. Idan haka ta samu kuma sai a fayyace rabe-raben bukukuwa a zamantakewar Hausawa a jiya da yau.

Ma'anar Buki

gyara sashe

Masana da daliban ilmi da dama sun bayyana ra'ayinsu dangane da maganar buki kamar a yada bayanai za su biyo nan gaba, misali Bichi (2'13:695) cewa ya yi kuma “Bukin gargajiya dole ya kasance na jama'a, mai sau}in gudanarwa wanda zai kawo annashuwa da jin dadi ga al'umma, Don haka kuma, bukin gargajiya ya kasance ana gudanar da shi ne a gargajiyance domin inganta al‟adu da aka gada kaka da kakanni” Maganar tana tabbatar mana da cewa a kowane bukin gargajiya dole ya zamana ana yin sa domin kare martabar al'adun mutane.[1]

1- A ra'ayin Smith (1976:160) ya bayyana buki A matsayin wasu al'adu na musamman wanda yake da kunshe da Karin maganganu da wakoki da kuma raye-raye” A 'a‟ayin Yahaya (2008:95) ya ce “ Buki wata hanya ceta gane irin karkashi da jin dadin da mazauna wani wuri suke yi ko ji na al‟adunsu da suke gudanarwa.”[2]

2- A fahimtar Gusau (2012:26) yana ganin buki “ A matsayin wani taro ne na mutane da suke shiryawa, su gudanar don nuna farin cikinsu a kan wata baiwa da Allah ya yi ma wani daga cikinsu, ko ya yi wa wasunsu” A kamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006:46) an bayyana buki da cewa “Shagali na nuna farin ciki wajen aure ko suna ko na]in sarauta ko sallah ko al'adun gargajiya” Dangane da ra'ayoyin masana da aka kawo a sama za a ga cewa ana aiwatar da buki ne a lokacin da wani abu ya faru ya faru na farin ciki domin baje kolin al'adu.[3]

Dalilan Buki

gyara sashe

Akwai dalilai da dama da ke haddasa aiwatar da buki ko bukukuwa a cikin al'ummar Hausawa kamar yadda muka ga wasunsu su bayyana a cikin ma‟anar da aka bayar ta buki. Ka]an daga cikin wadannan dalilai kuwa sun hada da;

  • Domin a martaba al‟adu: Irin wa]annan bukukuwa sun shafi bukin da ake musamman shehaka-shekara domin tunanwa da wasu muhimman al'adu da ake aiwatarwa.
  • Domin a samar da nishadi: A wasu lokuta akan shirya wasanni a cikin buki saboda a samar da nishadi ga halarta bukin.
  • Domin a nuna farin cikin faruwar wani abu mai muhimmanci a cikin al‟umma, misali bukin mauludi da ake gudanarwa a fadin kasar Hausa da ma wasu sassa na kudancin Nijeriya.
  • Ana aiwatar da bukukuwa ne domin murnar zagayowar shekara, misali bukin cika ciki ko kamun shara a tsakanin Hausawa.
  • Wani bukin ana yin sa domin murnar aure ko haihuwa ko na]in sarauta da askinta.
  • Buki kan faru a dalilin makokin mutuwa tun a jiya da kuma yau da Hausawa suka shaki iskar musulunci da zamunanci.
  • Buki kan faru a sakamakon kammalawa karatun addini ko boko, misali bukin saukar karatun Alkur‟ani day aye ]alibai a kwalejoji da cibiyoyin ilmi.
  • Hausawa sukan aiwatar da buki domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar `ya`yansu ko shugabanninsu, misali Mauludin Nabiyu.
  • Hausawa kan yi buki domin yi wa „ya‟yansu kaciya, musamman idan suka warkebayan sati biyu da yin kaciyar.
  • Ana yin buki a dalilin aiwatar da wasannin noma da ake yi shekara-shekara a gonar Sarakuna.
  • Hausawa suna yin buki a lokacin shagulgulan sallah babba da karama. A nan sukan baje kolin al‟adunsu na dambe, kokawa da tsiren dawaki ko kekuna da masuna.

Rabe-Raben Bukukuwan Hausawa

gyara sashe

Bukukuwa a kasar Hausa ana yi masu kallo a matakai guda uku muhimmai kamar haka;

Bukukuwan Hausawa na Gargajiya

gyara sashe

Bukukuwan Gargajiya; Wa]annan su ne da suka samo tushe daga tsarin bautar Hausawa ta gargajiya, irin wa]annan bukukwa a kodayaushe za a ga ~ir~ishin tsafi ko bori ko kuma camfi a cikinsu. Ma‟ana babu yadda za a yi a aiwatar da su ba tare da an ga nason tsafe-tsafen Hausawa na yanka dabbobi ga Iskoki ko wata hidima zuwa ga Iska domin a sami biyan bu}atar rayuwa na samun rowan sama ko damina mai albarka ko kariya daga wata cuta. Kadan daga cikin irin waɗannan bukukuwan sun haɗa da;

  • Bukin bukin dawa
  • Bukin shan kabewa
  • Bukin fashin ruwa
  • Bukin gyaran ruwa.

Bukukuwan Hausawa Bayan zuwan Musulunci

gyara sashe

Bukukuwan Hausawa bayan zuwan musulunci a kasar Hausa. Bayyanar Musulunci ga Hausawa da kuma kar~ar musuluncin da suka yi ya haifar masu da kirkiro wa kansu sababbin bukukuwa da za su dace da sabon addininsu na musulunci. A rayuwarsu ta addinin gargajiya, suna aiwatar da bukukuwan da suka shafi bauta da kuma nuna murna ga zagayowar wani abu mai muhimmanci, misali bukin juya kafa]a idan wani dattijo ya mutu suna aiwatar da bukin cika shekara daya da mutuwa da musulunci ya shiga zukatan Hausawa sai suka lura da cewa akwai wasu bukukuwa masu kama da nasu na gargajiya wa]anda ake aiwatarwa a shekara-shekara, misali bukin sallah da mauludi ya zama ɗaya daga cikin sababbin bukukuwan Hausawa.

Bukukuwan Hausawa Bayan zuwan Turawan Mulkin Mallaka

gyara sashe

Bukukuwan Hausawa Bayan zuwan Turawan Mulkin Mallaka: Waɗannan bukukuwa ne da suke ]auke da sabon tunani ga al‟adun zamantakewar Hausawa. Don haka, ake yi masu suna da sababbin bukukuwan zamani na Hausawa. Yi masu wannan sunan ba zai rasa nasaba da ganin asali Hausawa ba su da ire-iren waɗannan bukukuwa a cikin al‟adunsu. Misali akwai Fati (party), Fikinin (Picnic) da Lunching da ake yi musamman a lokacin auren Hausawa a yau inda samari da `yanmata sukan ke~e a wani wuri na musamman kamar Otal ko a rafi ko gefen kogi su sheke ayarsu da raye-raye da ka]e-ka]e.wa]anda suka sa~a wa al‟adun Hausawa na asali.

Matsayin Buki a Al’ummar Hausawa

gyara sashe

Buki abu ne da yake da babban matsayi ba ga Hausawa kadai ba har ma da sauran al‟ummun duniya. Dalili kuwa al‟ada ce da ta ratsa kowace kabila a fadin duniya. Don haka, idan za a dubi farfajiyar da al‟adun bukukuwa suka mamaye a cikin al‟adun Hausawa sai a ce babu wani mataki na rayuwa da ba a samun buki a cikin matakan rayuwar Hausawa kama daga aure, haihuwa da kuma mutuwa. To abin tambaya a nan shi ne, wane matsayi Bahaushe ya bai wa buki a jiya da yau? Babban matsayin da Bahaushe ya bai wa lamarin buki a cikin al‟adunsa shi ne domin cika wani umurni na tsarin bautarsa ta gargajiya da kuma addininsa na Musulunci. Wannan matsayin shi ya haifar da samuwar rabe-raben bukukuwan da aka tattauna a sama. Wani matsayin da ake iya gani ga bukin Hausawa bai wuce na samar da nishaɗi da kuma kulla zumnuta a tsakanin mutane ba. Misali bukin wasan bori da dangoginsa.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Bichi A.Y (2013). Tsokaci a Kan Bukukuwan Hausawa na Gargajiya wajen cigaban Al'umma. Zaria. Ahmadu Bello University, Press.
  2. Gusau G.U (2012). Bukukuwan Hausawa. Gusau: Ol-Faith Prints
  3. CNHN (1981). Rayuwar Hausawa. Lagos. Thomos Nilson Nigeria Limited.
  4. CNHN (2006) {amusun Hausa