Buhari Abdullahi Aliyu
Buhari Abdullahi Aliyu (An haife shi a shekara ta 1995) a wani garin Kwarin Ziri dake a Karamar hukumar Gwarzon Jihar Kano.
Buhari Abdullahi Aliyu | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | researcher (en) |
Karatu
gyara sasheBuhari ya fara karatun Firamari a shekarar 2002-2008 a Unguwar Na'ibi primary school. Sannan ya cigaba da karamar secondary a shekarar 2008-2011 a Karamar sakandare dake garin Kara.
Daga nan ya samu nasarar cigaba da karatun babbar sakandare a kwalejin kimiya dake Gaya a shekarar 2011-2014. Bayan nan ya samu gurbin karatu a tsangayar kimiya a Jami'ar Bayero dake Kano a shekarar 2015-2019. Inda ya samu shedar kammala digirin farko a (Bsc. Physics) Inda ya fita da darajar farko.
Daga nan ya samu tafiya kasar Indiya domin karo karatun digiri na 2. A sakamakon tallafin daya samu daga gidauniyar kwankwasiyya a shekarar 2019-2021. [1]
Yanzu haka dai Buhari yana hidimtawa kasa a jigawa polytechnic dake jihar Jigawa.