Black Star International Film Festival

Bikin fina-finai na Black Star International (BSIFF) bikin mara riba (non-profit festival) ne a Ghana wanda Juliet Asante ta kafa a cikin shekarar 2015. Biki ne da ake yi duk shekara domin cike gibin da ke tsakanin fina-finan Afirka da al'ummar duniya masu yin fina-finai da kuma mayar da hankali kan harkokin kasuwanci na shirya fina-finai.[1][2][3]

Infotaula d'esdevenimentBlack Star International Film Festival
Iri film festival (en) Fassara
Validity (en) Fassara 2015 –
Wanda ya samar Juliet Asante
Wuri Accra
Ƙasa Ghana

Yanar gizo bsiff.org

Ana yin bikin na mako guda kuma an haɗa shi da ayyuka da yawa waɗanda suka haɗa da Workshop, Panel Session, Kasuwar Fim ta Afirka, Kayan kiɗe-kiɗe, Kyaututtuka da kuma nuna fina-finai na yau da kullun. A lokacin waɗannan ayyukan masu halarta ko 'yan wasan masana'antu suna yin kasuwanci kuma suna murna da' yan Afirka don ayyukansu a cikin shekara.[4][5]

Jerin jigo daga shekarar kafuwar zuwa yau

Jigo Shekara
Siffata Tunanin Zamani 2016
Ga Matasa A Zuciya 2017
Fim A Matsayin Kayan Aikin Ci Gaban Ƙasa 2018
Haɗa Al'adu Ta Fim 2019

Manazarta

gyara sashe
  1. "BSIFF". Black Star International Film Festival (in Turanci). Retrieved 2020-04-13.
  2. "Black Star International Film Festival 2018 opens in Accra". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana, Current Affairs, Business News , Headlines, Ghana Sports, Entertainment, Politics, Articles, Opinions, Viral Content (in Turanci). 2018-08-14. Retrieved 2020-04-13.
  3. "Government to include Black Star International Film Festival in 2019 budget – Catherine Afeku". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-04-13.
  4. "Black Star International Film Festival". FilmFreeway (in Turanci). Retrieved 2020-04-13.
  5. "Black Star International Film Festival 2018 opens in Accra". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-04-13.