Bilal Yasin ( Urdu: بلال یاسین‎; an haife shi a ranar 14 ga watan Disamba, Shekarar 1970) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab daga watan Agustan 2018 har zuwa watan Janairun 2023. Ya kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab kuma tsohon memba na majalisar ministoci, daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018. Ya taɓa zama memba a majalisar dokokin Pakistan daga shekarar 2008 zuwa ta 2013. A cikin watan Disambar 2021 an harbe Bilal, kuma an kama dukkan waɗanda ake zargin.

Bilal Yasin
Member of the Provincial Assembly of the Punjab (en) Fassara

15 ga Augusta, 2018 -
District: PP-150 Lahore-VII (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Lahore, 14 Disamba 1970 (53 shekaru)
Karatu
Makaranta University of the Punjab (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara
Beautiful view of Punjab Assembly Lahore - panoramio.jpg
Punjab Majalisar Lahore

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haife shi a ranar 14 ga watan Disambar shekarar 1970 a Lahore[1][2] ga Yasin Pehalwan wanda ɗan uwan Kulsoom Nawaz ne.[3]

 

Ya kammala karatu a shekarar 1990 daga Jami'ar Punjab kuma yana da digiri na farko na Arts .[2]

Harkokin siyasa

gyara sashe

An zaɓe shi a Majalisar Lardi na Punjab daga Mazaɓar PP-139 (Lahore-III) a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-N) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002 .[4][5][6] Ya samu ƙuri'u 17,171 sannan ya doke Chaudhry Muhammad Asghar ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP).[7]

An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan daga Mazaɓar NA-120 (Lahore-III) a matsayin ɗan takarar PML-N a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 .[8][9][10] Ya samu ƙuri'u 65,946 ya kuma doke Jehangir Bader .[11]

An sake zaɓen shi a Majalisar Lardin Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-139 a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 .[12][13] Ya samu ƙuri'u 44,670 sannan ya doke Mazhar Iqbal ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).[14] A cikin watan Yunin 2013, an shigar da shi cikin majalisar ministocin lardi na babban minista Shahbaz Sharif kuma an naɗa shi ministan abinci na lardin Punjab.[15]

Bilal Yasin

An sake zaɓen shi a Majalisar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-150 (Lahore-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .[16]

Manazarta

gyara sashe
  1. "If elections are held on time…". www.thenews.com.pk (in Turanci). Archived from the original on 5 December 2017. Retrieved 4 December 2017.
  2. 2.0 2.1 "Punjab Assembly". www.pap.gov.pk. Archived from the original on 14 June 2017. Retrieved 18 January 2018.
  3. Reporter, The Newspaper's Staff (9 May 2012). "Yasin Pehalwan passes away".
  4. "LAHORE: Candidates declare poll expenses". DAWN.COM (in Turanci). 20 October 2002. Archived from the original on 7 April 2017. Retrieved 27 July 2017.
  5. "Speaker accepts 44 resignations: Notice to three MPAs". DAWN.COM (in Turanci). 5 October 2007. Archived from the original on 19 January 2018. Retrieved 27 July 2017.
  6. "Punjab Assembly". www.pap.gov.pk. Archived from the original on 21 January 2018. Retrieved 20 January 2018.
  7. "2002 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 January 2018. Retrieved 25 May 2018.
  8. "Sharifs constituency NA-120 in total neglect". www.thenews.com.pk (in Turanci). Archived from the original on 19 January 2018. Retrieved 27 July 2017.
  9. "As Pakistan goes to polls: Take a peek at some major NA constituencies". DAWN.COM (in Turanci). 10 May 2013. Archived from the original on 5 March 2017. Retrieved 27 July 2017.
  10. "PML-N Recaptures Lahore". DAWN.COM (in Turanci). 19 February 2008. Archived from the original on 7 April 2017. Retrieved 27 July 2017.
  11. "2008 election result" (PDF). ECP. Archived (PDF) from the original on 5 January 2018. Retrieved 25 May 2018.
  12. "Sewage, garbage heaps, open manholes: welcome to NA-120". www.thenews.com.pk (in Turanci). Archived from the original on 19 January 2018. Retrieved 27 July 2017.
  13. "List of winners of Punjab Assembly seats". The News (in Turanci). 13 May 2013. Archived from the original on 16 January 2018. Retrieved 18 January 2018.
  14. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 25 May 2018.
  15. Reporter, The Newspaper's Staff (11 June 2013). "21-member Punjab cabinet takes oath". DAWN.COM. Archived from the original on 22 January 2018. Retrieved 21 January 2018.
  16. "Pakistan election 2018 results: National and provincial assemblies". Samaa TV. Archived from the original on 2018-07-29. Retrieved 3 September 2018.