Sarakuna da mutanen gundumar Fanteakwa da ke yankin Gabashin Ghana suna yin bikin Odwira. Mutanen Akropong-Akuapim, Aburi, Larteh da Mamfi suna yin bikin Odwira. Ana yin wannan bikin kowace shekara a cikin watan Satumba. Bikin yana murnar nasarar tarihi akan Ashanti a 1826.[1] Wannan shine yakin Katamansu kusa da Dodowa.

Infotaula d'esdevenimentBikin Odwira
Iri biki
Wuri Akropong (en) Fassara
Ƙasa Ghana

Wannan shine lokacin mulkin Okuapimhene na 19 na Akropong, Nana Addo Dankwa 1 daga 1811 zuwa 1835. Lokaci ne na tsarkakewa ta ruhaniya inda ake sabunta mutane kuma suna samun kariya. Haka kuma mutanen Jamestown a Accra suna yin bikin. Wannan ya faru ne saboda ƙungiyoyin da aka kafa ta hanyar aure tsakanin mutanen Ga da Akuapem.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. "Odwira Festival". Retrieved July 3, 2012.
  2. "The Odwira Story". Akropong Akuapem Odwira Festival (in Turanci). Retrieved 2020-11-05.