Bikin Ƙasa da Ƙasa na Hammamet

Hammamet International Festival biki ne na kaɗe-kaɗe da fasaha na shekara-shekara a birnin Hammamet da ke gaba da teku a ƙasar Tunisiya.[1] An kafa shi a cikin shekarar 1964 kuma ana gudanar da shi a watan Yuli da Agusta a cikin filin wasan amphitheater mai kujeru 1000 da ke kallon Tekun Hammamet.[1] Ma'aikatar Al'adu ce ta shirya shi wannan bikin na shekar shrkara, wanda ke gudana da kuma naɗa darekta. Tun daga shekarar 2014, Cibiyar da bikin suna ƙarƙashin jagorancin Kamel Ferjani.[2] A cikin shekarar 1980s, Ute Lemper, Mikis Theodorakis, Miriam Makeba sun bayyana, kuma kwanan nan, Victoria Abril, Emir Kusturica, Tina Arena, Anouar iBrahem, Raouf Ben Yaghlane, Leila Hjaiej da ƙungiyar rap na Farasa IAM4 sun bayyana.

Hammamet International Festival

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Wheeler, Donna; Clammer, Paul; Filou, Emilie (2010). Tunisia. Lonely Planet. p. 284. ISBN 978-1-74179-001-6.
  2. "Kamel Ferjani: Gloria Gaynor et Cheb Mami programmés exclusivement au festival d'Hammamet" (in French). Mosaiquefm.net. Archived from the original on 4 August 2015. Retrieved 5 June 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)