Ben-Collins Ndu

Dan siyasa ne a Najeriya

Ben-Collins Ndu (an haife shi a ranar 6 ga Nuwamba 1961) an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta Yamma ta Jihar Enugu, Najeriya a watan Maris na 2001 yana neman tsayawa takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).[1]

Ben-Collins Ndu
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Maris, 2001 - Mayu 2003
Hyde Onuaguluchi (en) Fassara
District: Enugu West
Rayuwa
Haihuwa Ezeagu, 6 Nuwamba, 1961 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
sanetar Ben-Collins Ndu
hoton sanata ben

Ndu dan asalin karamar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu. Ya kasance dan takara a zaben da aka yi a watan Afrilun 1999 na dan majalisar dattawan Enugu ta Yamma, inda ya fafata da Reverend Hyde Onuaguluchi na jam’iyyar All People’s Party (APP), amma aka ayyana Onuaguluchi a matsayin zababben gwamnan. Ndu ya shigar da kara gaban kotun zabe bisa cewa an tafka magudi kuma an tafka kura-kurai wajen gudanar da zaben a kananan hukumomin Awgu da Aninri . Bayan an daɗe ana fafatawa shari’a, a watan Maris na shekara ta 2001, Kotun Koli ta soke zaɓen Onuaguluchi kuma ta ba da umarnin sake yin sabon zaɓe.[2]

Ndu ya cigaba da zama zababbe a kujerar Sanatan Enugu ta Yamma. An nada shi shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar zabe mai zaman kanta. Kafin zaben Afrilu 2003, Ndu ya yi takun-saka da Gwamnan Jihar Enugu Chimaroke Nnamani. Jam'iyyar PDP ta zabi Ike Ekweremadu, shugaban ma'aikatan gwamnan a matsayin dan takarar su na Enugu ta yamma kuma ya ci zabe. [3]

A ranar 31 ga Yuli, 2013, an sanar da cewa an nada Ben-Collins Ndu Shugaban Cibiyar Gudanar da Fasaha ta Kasa.

Manazarta

gyara sashe

Samfuri:Nigerian Senators of the 4th National Assembly