Beatrice Sandelowsky
Beatrice Sandelowsky (an haife ta a shekara ta 1943) ƙwararriyar masaniya ce a fannin ilimin kimiyya na kayan tarihi ta ƙasar Namibiya.[1] Ta kasance mai haɗin gwiwa na Cibiyar Nazarin Jami'ar Namibia (TUCSIN).[2]
Beatrice Sandelowsky | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Namibiya, 1943 (80/81 shekaru) |
ƙasa | Namibiya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Cape Town |
Sana'a | |
Sana'a | archaeologist (en) da scientist (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheSandelowsky ta girma a gonar iyayenta da ke Brakwater kusa da Windhoek.[1] Ta yi makarantar sakandare a Swakopmund, kuma bayan kammala karatunta, ta ci gaba da karatunta a Jami'ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu inda ta sami takardar shaidar koyarwa. Daga nan ta sami BA a Jami'ar Rochester da ke New York sannan ta sami digiri na uku a fannin ilimin kimiya na kayan tarihi daga Jami'ar California a Berkeley a shekarar 1972.[3][4]
Sandelowsky ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga cikin kafa Cibiyar Ilimi ta Rössing Foundation da Ƙungiyar Tarihi na Namibia (MAN). A cikin shekarar 1978 ta kasance mai haɗin gwiwa na Cibiyar Nazarin Jami'ar Namibia (TUCSIN) kuma daga baya ta zama ɗaya daga cikin masu gudanarwa.[2] Ta kuma ba da gudummawa ga Gidan Tarihi na Rehoboth da Laburaren Jama'a na Rehoboth.[1] Daga shekarun 1988 zuwa 2000 ta yi aiki a matsayin memba na Hukumar Zaɓe ta Namibia (ECN) kuma ta kasance mamba a Majalisar Al'adun gargajiya ta Namibia har zuwa shekara ta 2006.[1]
Wallafe-wallafe
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 "Beatrice Sandelowsky: A Decorated Archaeologist, Educationalist and Agitator for Equality (1943 …)". Truth, for its own sake. (in Turanci). Retrieved 2022-06-24.
- ↑ 2.0 2.1 "TUCSIN - The University Centre for Studies in Namibia - Deed of Trust". www.tucsin.org. Archived from the original on 2022-05-26. Retrieved 2022-06-24.
- ↑ Campbell, Elizabeth; Webb, Karen; Ross, Michelle; Hudson, Heather; Hecht, Ken (2015-04-02). "Nutrition-Focused Food Banking". NAM Perspectives. 5 (4). doi:10.31478/201504a. ISSN 2578-6865.
- ↑ Lee, Richard (2013). "Beatrice Sandelowsky, Director of TUCSIN, at the launch of the TUCSIN training centre at the Tsumkwe Lodge. Image 2" (in Turanci). University of Toronto.
- ↑ Sandelowsky, Beatrice (2004). Archaeologically Yours, Beatrice Sandelowsky: A Personal Journey Into the Prehistory of Southern Africa, in Particular Namibia (in Turanci). Namibia Scientific Society. ISBN 978-99916-40-57-0.
- ↑ "Archaeologically yours. A personal journey into the prehistory of Southern Africa/Namibia im Namibiana Buchdepot". www.namibiana.de. Retrieved 2022-07-23.
- ↑ "Prehistory in the Central Namib Desert im Namibiana Buchdepot". www.namibiana.de. Retrieved 2022-07-23.