Alhaji Bashir Adewale Adeniyi (MFR) shi ne Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya. Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa ta Memba na Jamhuriyyar Tarayya (MFR) a ranar 11 ga Oktoba, 2022.

Bashir Adewale Adeniyi
Rayuwa
Sana'a

Adeniyi ya shiga ma’aikatar kwastam ta Najeriya, ya zama mataimakin kwanturolan kwastam a shekarar 2012, sannan ya riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a ƙasa baki ɗaya (Hedikwatar Abuja) da sauran ayyuka.[1]

An naɗa shi Kwanturolan Kwastam a watan Afrilun 2017, daga baya an sake naɗa shi a matsayin mataimakin kwamandan hukumar kwastam da ma'aikatan kwalejin Gwagwalada, Abuja.

Adeniyi ya zama Mataimakin Kwanturola Janar a watan Fabrairun 2020, kuma ya sa ido a kan kama wasu kuɗaɗe da suka kai dalar Amurka miliyan 8.07 da ake fitsrwa daga Najeriya ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar E-Wing na kwalta na filin jirgin sama na kasa da kasa.[2] A watan Janairun 2023, ya zama Muƙaddashin Mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) sannan kuma a watan Yunin 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi muƙaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS).[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "All you need to know about Adewale Adeniyi, the new Acting Customs CG - Ships & Ports" (in Turanci). 2023-06-20. Retrieved 2023-10-10.
  2. Anagor-Ewuzie, Amaka (2023-06-21). "From image making to CG, meet Adewale Adeniyi new Customs boss". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2023-10-10.
  3. "Seven things about Adeniyi, acting Customs CG who seized $8m at Lagos airport". Daily Trust (in Turanci). 2023-06-19. Retrieved 2023-10-10.