Balghis Badri (Larabci: بلقيس بدرى, an haifeta a shekara ta 1948) yar gwagwarmayar mace ce 'yar kasar Sudan, musamman a fagen kaciyar mata (FGM) da kuma ci gaban matan karkara, tun daga shekara ta 1979, kuma farfesa a fannin ilimin halayyar dan adam a Jami'ar Ahfad don Mata .

Balgis Badri
Rayuwa
Haihuwa 1948 (75/76 shekaru)
Karatu
Makaranta University of Hull (en) Fassara
Jami'ar Ahfad ta Mata
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam

Rayuwarta ta farko

gyara sashe

Ahalinta sun kasance masu illimi ne. sannan ita 'yace ga Yusuf Badri, wanda shine yasamar da Ahfad University for Women (AUW) a Khartoum a shekara ta1966, sannan jika ce ga Mahdist soja, Babiker Badri.[1]

Badri ta sami digirin digirgir a fannin ilimin halayyar dan adam daga Jami'ar Hull da ke Ingila a shekara ta 1978.

Sana'arta

gyara sashe

Badri ta kasance malamar wucin gadi a Jami’ar Mata ta Ahfad daga shekara ta 1974 zuwa shekara ta 1997, kuma tana aikin cikakken lokaci tun daga lokacin, inda a yanzu ta zama farfesa a fannin nazarin zamantakewar al’umma. A shekara ta 2002 ta kafu kuma ta zama darekta na farko na Cibiyar Nazarin Mata, Jinsi da Ci gaban AUW. [1] Badri ita ce Darakta na Jami'ar Ahfad don Cibiyar Mata ta Yanki na Gender, Diversity, Peace and Rights, a Omdurman / Khartoum . [1] A cikin shekara ta 1979, ta gabatar da mata da karatun da suka shafi jinsi a cikin manhajojin jami'a.

Rubutunta

gyara sashe

A cikin Fabrairu shekara ta 2017, Ayyukan Mata a Afirka (wanda Badri da Aili Mari Tripp sukayi tare) Zed Books ne suka buga. Badri ta hada shi, kuma ta rubuta guda biyu cikin babi goma. [2]

Rigimarta

gyara sashe

A watan Janairun shekara ta 2018, an nada dan uwan Badri, Gasim Badri, shugaban jami'ar mata ta Ahfad, a faifan bidiyo yana kama wata daliba, wacce ke zanga-zangar, da gyalenta, ta kuma yayi mata mari a kai. Badri dai ya kare matakin da ya dauka yana mai cewa faifan bidiyon ya nuna gaskiya daya ne kawai kuma wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi barazanar cutar da jami'ar.

  1. 1.0 1.1 1.2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named norad.no
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named uchicago.edu