Bahir Dar Kenema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa
Bahir Dar Kenema Football Club (Amharic :Bahardar da kema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa) ana kuma kiransa da Bahir Dar City, Kulab ɗin kasan Habasha ne dake birnin Bahir Dar. Suna taka leda a gasar firimiya ta Habasha, babban rukuni na ƙwallon ƙafa a Habasha.
Bahir Dar Kenema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Habasha |
Mulki | |
Hedkwata | Baher Dar |
bahirdarkfc.com |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Tarihi
gyara sasheAn kafa Bahir Dar Kenema a shekarar 1973 a birnin Bahir Dar.
Bahir Dar ta samu kyakyawan matsayi a kakar wasa ta 2017-2018 tana jagorantar rukunin A na babbar gasar Habasha da maki 31 bayan mako na 14.
A ranar 29 ga watan Yulin 2018 kungiyar ta samu nasarar shiga gasar firimiya ta kasar Habasha a karon farko a tarihinta bayan da ta doke kungiyar Inshora ta Habasha Nasarar ta tabbatar mata da matsayi na daya a rukunin A a gasar Higher League ta Habasha (a mataki na biyu) da saura wasanni uku. a kakar wasa ta 2017-18, ta hanyar tabbatar da matsayinsu a cikin babban lig a kakar wasa ta gaba.
A ranar 6 ga watan Agusta 2018 kungiyar ta sanar da tsawaita kwantiragin Paulos Getachew har zuwa kakar wasa ta 2018-19.
Filin wasa
gyara sasheBahir Dar Kenema sun buga wasansu na gida a filin wasa na Bahir Dar International Stadium . Sun raba filin wasan da Amhara Weha Sera, wani kulob da ke Bahir Dar.
Taimako
gyara sasheBahir Dar Kenema na da dumbin magoya baya inda magoya bayan kungiyar ke yawan tafiya tare da kungiyar a lokacin wasannin waje.
Sassan
gyara sasheSassan Ayyuka
gyara sashe- Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata
'Yan wasa
gyara sasheTawagar farko
gyara sasheTun daga Maris 7, 2021
|
|
Jami'an kulab
gyara sasheMa'aikatan Koyarwa
gyara sasheHar zuwa Maris 7, 2021