Badarawa
Badarawa, Babban anguwa ce dake Kaduna karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa.[1][2][3][4] wanda take kewaye da unguwanni kamar haka, daga kudu Unguwan Sarki unguwar rimi, da kuma Unguwan Dosa daga Arewa da Unguwan Kanawa daga yamma (Nigerian Defence Academy), sai Malali daga gabas duk acikin garin Kaduna.[5] Tanada kananan unguwanni kamar su: Kwaru, Malali, Majalisa, Unguwan Yaro, Unguwan Shekara da Unguwan Mai Samari.[6] Duk da Badarawa ta kasu gida biyu ne, birnin Badarwa kamar su Wurno Road, Ogbadu Street da kuma kauyan Badarawa kamar su Kwaru, Majalisa, Ƙaraye Road.[7][8] Unguwan na da makaranta L.E.A firamare, ana kiranta L.E.A Badarawa 1 da Badarawa 2, inda yaran gari ke gudanar da karatunsu na zamani. A yanzu ta Kara samun habaka na samun gaba da sakandare na jeka ka dawo, wanda akafi saninta da "Day Bola" [9]
Badarawa, | ||||
---|---|---|---|---|
ward of the Kaduna North legislative council (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Kaduna | |||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Kaduna ta Arewa |
Shuwagabanni
gyara sasheTana da shuwagabanni guda biyu daya ana kiranshi Mai-anguwa ko Sarkin Badarawa da kuma zababban shugaba na damakwaradiya mai suna Kansila.
Hadin waje
gyara sashe- Kaduna State Media Corporation Archived 2019-01-23 at the Wayback Machine
- Official State Government Website Archived 2019-12-10 at the Wayback Machine
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Badarawa in Kaduna North - Kaduna - CityDir.org". www.citydir.org. Retrieved 2019-12-14.
- ↑ "Badarawa Main Road, Kaduna, Nigeria". ng.geoview.info. Retrieved 2019-12-15.
- ↑ "Google Maps". Google Maps (in Turanci). Retrieved 2019-12-15.
- ↑ "Energy | Badarawa PHC" (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-15. Retrieved 2019-12-15.
- ↑ "Badarawa Polling Units". www.manpower.com.ng. Retrieved 2019-12-14.
- ↑ "Driving Directions Map to 7, Dutse Road Badarawa Kaduna, Ungwan Boro, Kaduna North for Biz Id 359757 | VConnect™". m.vconnect.com. Retrieved 2019-12-14.[permanent dead link]
- ↑ "PostCode !". web.archive.org. 2009-10-07. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2019-12-14.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "iFollowTheMoney". iFollowTheMoney (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-14. Retrieved 2019-12-14.
- ↑ "iFollowTheMoney". iFollowTheMoney (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-14. Retrieved 2019-12-14.