Bacillus anthracis kwayar cuta ce ta gram-positive kuma mai siffar sanda wacce ke haifar da cutar anthrax, cuta mai saurin kisa ga dabbobi kuma, lokaci-lokaci, ga mutane. Ita ce kadai cuta ( wajabta ) a cikin kwayar halittar Bacillus. Kamuwa da cuta yana faruwa ta hanyar dabbobine ne, kamar yadda ake yada shi daga dabbobi zuwa mutane. [1] Wani likita dan kasar Jamus Robert Koch ne ya gano ta a shekara ta 1876, kuma ya tabattar da cewa itace kwayar cuta ta farko da aka nuna ta hanyar gwaji. Binciken kuma shine shaidar farko ta kimiyya don ka'idar da ta nuna cewa akwai ƙwayoyin cuta . [2]

Bacillus anthracis
Scientific classification
KingdomBacillati (en) Bacillati
PhylumBacillota (mul) Bacillota
ClassBacilli (mul) Bacilli
OrderCaryophanales (mul) Caryophanales
DangiBacillaceae (mul) Bacillaceae
GenusBacillus (mul) Bacillus
jinsi Bacillus anthracis
,
General information
Rashin lafiya ANTRAX (en) Fassara
Gram stain gram-positive bacteria (en) Fassara
Bacillus anthracis plate
Anthrax

B. Anthracis wanda ba a yi maganinta ba yawanci yana iya saka mutuwa. Alamar kamuwa da cuta ya hada da kumburi, baƙar fata, raunin necrotic ( eschars ). tabon yakan bayyana akan fuska, wuya, hannaye. Alamun cututtuka sun haɗa da zazzabi mai kama da mura, rashin jin daɗin ƙirji, diaphoresis (yawan zufa), da ciwon jiki. Wani masanin kimiyar Faransa Louis Pasteur ne ya samar da allurar rigakafin dabbobi ta farko a kan anthrax a shekara ta 1881. Ana samun alluran rigakafin dabbobi da na mutane daban-daban yanzu. Ana iya magance cutar ta hanyar maganin rigakafi na yau da kullun kamar penicillins, quinolones, da tetracyclines.

Tarihinta

gyara sashe

Likitan Faransa Casimir Davaine (1812-1882) ya nuna alamun anthrax sun kasance koyaushe tare da kwayar cutar B. anthracis . [3] Likitan Jamus Aloys Pollender (1799-1879) an bashi yabo shi don ganowa. B. anthracis ita ce kwayar cuta ta farko da aka tabbatar da ita tana haifar da cuta, ta Robert Koch a 1876. [4]

Sunan nau'in anthracis ya fito ne daga anthrax na Girka (ἄνθραξ), ma'ana "kwal" kuma yana nufin mafi yawan nau'in cutar, cutaneous anthrax, wanda a cikinsa ya sami raunuka masu girma, baƙar fata. A cikin karni na 19, Anthrax kamuwa da cuta ne wanda ya haɗa da ci gaban kiwon lafiya da yawa. Alurar riga kafi na farko mai dauke da rayayyun kwayoyin halitta shine maganin cutar anthrax na dabbobi na Louis Pasteur. [5]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://pubmed.ncbi.nlm.nih.gov/12610093
  2. https://pubmed.ncbi.nlm.nih.gov/20413340
  3. "Reference genome: Bacillus anthracis str. 'Ames Ancestor'". NCBI Genomes. National Center for Biotechnology Information. February 13, 2022. Retrieved February 28, 2022
  4. https://doi.org/10.1002%2F9781118960608.gbm00530
  5. https://doi.org/10.1084%2Fjem.20161141