Baboucarr Gaye (an haife shi a ranar 24 ga Fabrairun shekarar 1998) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida/raga na FC Rot-Weiß Koblenz. An haife shi a Jamus, yana wakiltar tawagar ƙasar Gambia.

Baboucarr Gaye
Rayuwa
Haihuwa Bielefeld, 24 ga Faburairu, 1998 (26 shekaru)
ƙasa Gambiya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Arminia Bielefeld (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga
Tsayi 1.96 m
Baboucarr Gaye

Aikin kulob/Kungiya

gyara sashe

Bayan da ya yi amfani/aiki a matsayin sa na matashi tare da kulob ɗin Arminia Bielefeld, an sanar da cewa Gaye zai bar kulob ɗin a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2019, bai taɓa bayyana a cikin tawagar farko ba. A ranar 21 ga Yuli 2019, daga baya ya shiga SG Wattenscheid 09. [1] Bayan wasanni tara kacal, an tilasta wa Gaye ya nemo wani sabon kulob bayan Wattenscheid ya shigar da ƙara kan fatarar kuɗi a tsakiyar watan Oktoban 2019, inda suka rasa sauran kakar wasan su. [2] A cikin Janairu 2020, matashin mai tsaron gida ya shiga VfB Stuttgart II. [3]

A cikin watan Yulin shekarar 2020, Gaye ya koma TuS Rot-Weiß Koblenz. [4]

Ayyukan ƙasa

gyara sashe
 
Baboucarr Gaye a lokacin wasa
 
Baboucarr Gaye a cikin yan wasa

Gaye ya yi karo/haɗu da tawagar ƙasar Gambia a wasan sada zumunci da suka doke Congo da ci 1-0 a ranar 9 ga Oktoba 2020.

Bayanan kula

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • Baboucarr Gaye at DFB (also available in German)
  • Baboucarr Gaye at kicker (in German)
  • Baboucarr Gaye at WorldFootball.net