Azumi[1] shi ne kamewa[2] daga barin cin abinci ko sha ko jima'i (saduwan tsakanin namiji da mace) ko shan taba ko allura ta abinci daga ketowar alfijir nabiyu har zuwa faduwan rana. Hakika Allah ya wajabta azumi acikin Alkur'ani mai girma inda yace "duk wanda ya riski watan (Ramadan) to ya azumceshi" shi Musulmi ne (surah albakarah 2:185) sannan ya kara da cewa "ya ku masu imani hakika an wajabta muku azumi kamar yanda akawajabta ma wanda suke gabaninku koku zakuyi takawa" (albakarah 2:183) abubuwanda suke karya azumi #cin abinci

  1. shan abinsha
  2. jima'i
  3. shantaba
  4. abu maisa maye
  5. alluran abinci da dai sauran dukkan abinda zai bi ta makoshin mai azumi
Wikidata.svgAzumi
human behavior (en) Fassara
Fasting 4-Fasting-a-glass-of-water-on-an-empty-plate.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na abstinence (en) Fassara da food deprivation (en) Fassara
Amfani religious rite (en) Fassara, trance (en) Fassara, weight loss (en) Fassara da Azumi
WordLift URL (en) Fassara http://data.medicalrecords.com/medicalrecords/healthwise/fasting

Azumi akwai wanda yake wajibi akwai kuma na Nafila wato sunnah, Azumin wajibi wato na Farilla shine Azumin watan Ramadan, Azumin kaffara da kuma Azumin balance. Shi na Ramadan indai ya riski Musulmi yanada lafiya, da hankali, kuma baligi (Balaga) wanda ya ke mazaunin gida ma'ana ba matafiyi ba, kuma ba lokacin jinin al'ada ba ga mata ko kuma Jego ko kuma tsohon da tsufa yasa baya iya yin Azumi, ko kuma wani dalili mai ƙarfi wanda ma'abota Ilimin addinin Musulunci sukayi fatawa a kanshi. Sai Azumin Nafila kamar azumin Litinin da Alhamis sai kuma sauran azumin Nafila waɗanda suma sanannu ne. Sai azumin bakance shi ma wajibi ne, amma don sanin haka sai a tambaya Malaman Musulunci Masu riƙon sunnah waɗanda keyi don Allah. Ina ƙara nanata wa azumin watan Ramadan wajibi ne[3] don saboda haka Ayoyin Alqur'ani mai girma da sukayi nuni da hakan. Anason a lokacin Azumin watan Ramadan mutum ya yawaita Ibadu kamar yawan karatun Alqur'ani, sadaƙa, zumunta, Istigfari, yawan nafila musamman Sallah tarawihi Tahajjud da kuma kiyaye jam'i Sallolin Farilla da dai sauran Ibadu da shari'a ta bada umarnin yin su. Don ƙarin bayani akan Azumi a duba littafin (Iziyya da Risala).

ManazartaGyara