Aziza Baroud
Ammo Aziza Baroud (an haife ta ranar 4 ga watan Agusta, 1965) 'yar siyasar ƙasar Chadi ce wadda tayi aiki a matsayin Ministan Lafiya ta kuma rike muƙamin Wakiliyar Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya tun daga shekarar 2019.
Aziza Baroud | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | unknown value, 4 ga Augusta, 1965 (59 shekaru) | ||||
ƙasa | Cadi | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Baroud a ranar 4 ga watan agustan shekarar 1965.
A watan Satumba ta zama Ministar Lafiya a karkashin Shugaba Idriss Deby.
A shekarar 2019 ta kasance Jakadiyar Chadi a Tarayyar Turai, Ingila, da ƙasashen Benelux. A ranar 27 ga Disamban shekarata 2019 aka yi bikin tunawa da Moustapha Ali Alifei wanda ya kasance Wakilin Dindindin na Chadi a Majalisar Dinkin Duniya. Inda anan ne kuma shugaban kasa ya nada Baroud a hukumance don maye gurbinsa. Inda wajen zamanta ya kasance a New York.
A cikin 2020 yayin Coronavirus Pandemic Baroud na aikin taimaka wa Uwargidan Shugaban kasa Hinda Déby da Diego Canga Fano yayin da suke tattauna damar kasuwanci a Chadi tare da masu saka jari na Turai.