Ayo Oke
Ayo Oke shine tsohon babban darakta na hukumar leken asirin Najeriya (NIA), wanda shugaban kasa na wancan lokacin Goodluck Jonathan ya nada a ranar 7 ga Nuwamba 2013.
Ayo Oke | |||
---|---|---|---|
7 Nuwamba, 2013 - Oktoba 2017 | |||
Rayuwa | |||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Ayo Oke a jihar Oyo.
Ayyuka
gyara sasheOke ya taba zama Darakta (Yankuna) a hedikwatar hukumar ta NIA, kuma kafin hakan shi ne jakadan Najeriya a Sakatariyar Commonwealth da ke Landan. Ya gaji Ezekiel Olaniyi Oladeji a matsayin darekta janar na Hukumar Leken Asiri ta Najeriya a watan Nuwamban shekarar 2013.
Dakatarwa da sallama
gyara sasheA watan Afrilu na shekarar 2017, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Oke bayan da jami’an yaki da cin hanci da rashawa daga Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati suka gano sama da dalar Amurka miliyan 43 (£ 34m) a cikin wani gida a Osborne Towers, Ikoyi, Lagos . A ranar 30 ga Oktoba, daga karshe shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kori Oke bayan nazarin rahoton kwamitin binciken da Mataimakin Shugaban ya jagoranta. [1]
Bayani
gyara sashe- ^ a b
- ^
- ^
- ^
- ^ http://sunnewsonline.com/breaking-buhari-sacks-babachir-lawal-ayo-oke-appoints-mustapha-new-sgf/