Assin (wanda aka fi sani da Asin da Asen) ƙabila ne na ƴan Akan da ke zaune a Ghana. Mutanen Assin suna zama mafi yawa a yankin tsakiyar Ghana. Babban birnin gundumar Assin shine Assin Foso.

Assin
Jimlar yawan jama'a
135,000
Yankuna masu yawan jama'a
Ghana

Yanki gyara sashe

Akwai yankuna biyu na mutanen Assin. Assin Apemanim (ko Apimenem) suna zaune a gabas da babbar hanyar Cape Coast-Kumasi, tare da Manso a matsayin babban birninsu. Assin Attendansu (ko Atandanso) suna zaune a yammacin babbar hanya, tare da Nyankumasi a matsayin babban birninsu.

Yawa gyara sashe

A shekarar 1995, an kiyasta yawansu ya kai 135,000.

Manazarta gyara sashe