Asma'u Makarfi ta kasan ce matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, wato Ahmed Makarfi.

Farkon Rayuwa da Ilimi gyara sashe

Hajiya Asma’u Maƙarfi ta fara karunta na firamare a shekara ta alif 1977, a makarantar Kaduna Capital School. Inda ta fara samo wayewarta a kan harkar ilimi da ɗabi’a ta kula da yara. Ta kammala karatunta na firamare ba tare da wata tangarɗa ba a shekara ta 1983, inda ta samu shiga makarantar Queen Amina Kaduna, wadda ta kasance makarantar mata ce zalla. Ta kammala karantunta na sakandire ba tare da wata tangarɗa ba inda ta samu zarcewa zuwa ga babbar jami’ar Ahmadu Bello dake birnin zaria a shekara ta 1989, ta karanci Banking and Finance a matakin diploma. Sannan ta zarce ta yi digiri a kan Accounting and Finance duk a Jami’ar Ahmadu Bello a shekara ta 1997. Asma’u ta kammala karatunta kuma ta zarce kai tsaye wajen hidimar ƙasa, watau (NYSC) a shekarar ta alif 1998, a Jihar kaduna

Bibiliyo gyara sashe

  • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Manazarta gyara sashe