Asha Negi
Asha Negi, (an haife ta a ranar 23 ga watan Agusta na shekarar ta 1989) ’yar fim ɗin Indiya ce. An fi saninta da taka rawar da tayi a matsayin Purvi Deshmukh a cikin shahararren wasan kwaikwayo na tashar Zee TV Pavitra Rishta da kumawasan kwaikwayo na Star Plus. A shekarar 2019, ta fara yin shuhurarta a zamance da shirin Balaish Telefilms da aka samar da Baarish a matsayin Gauravi Karmakar inda ta kishiyanci Sharman Joshi.
Asha Negi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dehradun, 23 ga Augusta, 1989 (35 shekaru) |
ƙasa | Indiya |
Mazauni | Mumbai |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Rithvik Dhanjani (en) (2011 - |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da dan wasan kwaikwayon talabijin |
IMDb | nm4898167 |
Kuruciya
gyara sasheHaihuwar Negi da kuma girman ta duk a garin Dehradun, Uttarakhand ne. Iyayenta su ne Malam LS. Negi da Beena Negi. A shekarar 2009, an nadata sarauniyar kyau ta garin su Miss Uttarakhand 2009.[ana buƙatar hujja] A ƙarshe ta koma Mumbai don shiga harkar fim.
Rayuwar Iyali
gyara sasheNegi ta fara alaƙar soyayya da abokin aikinta da ya fito a matsayin Pavitra Rishta wato coster cikin shirin Rithvik Dhanjani da aka sake a shekarar 2013, amma sun rabu a cikin watan Mayun shekarata 2020.