Arne Slot
Arend Martijn "Arne" Slot (An haifeshi ranar 17 ga watan Satumba, 1978) Kwararren mai bada horo ne na ƙasar Dutch. Sannan kuma tsohon dan wasa wanda yanzu haka yake horas da Ƙungiyar kwallon kafa ta Liverpool.
Arne Slot | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Bergentheim (en) , 17 Satumba 1978 (46 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Kingdom of the Netherlands (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Dutch (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Dutch (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm14028180 |
Slot ya buga kwallo a matsayin dan wasan tsakiya a kungiyar F. C Zwolle inda yaci gasar Eeste Divisie a shekarar alif 2002 da NAC Breda da kuma Spata Rottedam. Kafin ya ajiye kwallon kafa ya dawo kungiyar PEC Zwolle inda ya ƙara cin wani kofin na gasar Eeste Divisie a shekarar alif 2012.
Ya fara yin rayuwa a matsayin mai bada horo a cikin akadami ta kungiyar kwallon kafa ta PEC Zwolle a matsayin mataimaki, daga baya kuma ya zama kocin ƙungiyar akademi din a shekarar alif 2017. Daga baya kuma ya zama mataimakin mai bada horo a ƙungiyar kwallon kafa ta AZ kuma ya zama kocin ƙungiyar a shekara ta alif 2019. Slot ya zama kocin ƙungiyar kwallon kafa ta Feyenoord a shekarar alif 2021. Ya jagoranci ƙungiyar har zuwa wasan ƙarshe na gasar UEFA Europa Conference. Ya cima ƙungiyar gasar Eridivisie da kofin KNVB duk a shekarar.
Rayuwa ta dan wasa
gyara sasheSlot ya fara buga wasa a ƙaramar ƙungiya ta VV Bergentheim daga garin Bergentheim wurin da aka haifeshi. Sannan ya matsa zuwa ƙungiyar kwallon kafa ta Zwolle kuma ya shiga cikin 11 din farko a shekarar alif 1995 lokacin yana dan shekara 17.
Slot ya fara rayuwar kwallon shi da matsaloli da yawa inda ya fuskanci matsala ta jin rauni da kuma karancin buga wasa a karkashin jagorancin Jan Everse, amma a hankali ya zama dan tsakiya mai cin ƙwallo a zwolle. A shekarar alif 2002 Zwolle ta ci kofin Eerste Divisie suka dawo gasar Divisie bayan shekaru 13. Slo[1]t ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta NAC Breda a wannan shekarar.[2]
A ƙarƙashin jagorancin Henk Ten Cate, NAC Breda sun kare a mataki na 4 a shekarar farko ta slot hakan babbar nasara ce ga kungiyar tun shekarar alif 1956. Slot ya buga wasan shi guda daya a gasar turai ta UEFA cup shekarar alif 2003. A gasar sunyi rashin nasara daci 5-0 da kuma 1-0 a wasa biyu da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United. Ya jona kungiyar sparta Rotterdam a bazara, shekarar alif 2007 kafin ya dawo kungiyar Zwolle a Eeste Divisie a shekarar alif 2009 a zaman aro da yaje. Kuma ya zama dan wasansu na dindindin a shekarar alif 2010. Kungiyar ta FC Zwolle ta lashe gasar Eeste Divisie a shekarar alif 2012 hakan ya basu dama suka dawo babbar gasar Eridivisie inda Slot ya buga wasan karshe kafin ya aje kwallo.
A yanda abokin aikin nashi yace, Edwin De Graab yace "Dan wasan beda sauri".[3]
Everse ma ya yadda cewa dan wasan yana da nawa amma mun gode da passing da kuma hikimar dan wasan.
Rayuwar Horaswa
gyara sasheRayuwar Farko
gyara sasheA cewar abokin aikin shi Bram van Polen, S[4]lot yana yin dabi'a irin ta masu bada horo a kungiyar PEC Zwolle a shekarar karshe a matsayin dan wasa. Bayan a ya ajiye kwallo a shekarar alif 2013 a kungiyar Zwolle, Slot ya shiga cikin masu ruwa da tsaki na cikin kungiyar. Slot ya zama daya daga cikin masu bada horo har ya zama wanda yafi kowane koci mai karancin shekaru na shekarar.[5]
Kafin ya zama mataimakin koci na kungiyar kwallon kafa ta Henk De Jong, Ya bar kungiyar a shekarar alif 2016. Slot ya cigaba da zama mataimakin mai bada horo a kungiyar kwallon kafa ta Ciambuur a karkashin jagorancin Marcel Keizer da Rob Maas. Kungiyar ta yi rashin nasarar tsallakawa gasar Eeste Divisie bayan da suka kare a kasan Teburi na gasar Eridevisie a shekarar alif 2016.[6]
A ranar 15 ga watan Oktoba 2016, Slot ya zama mai bada horo a kungiyar kwallon kafa ta Interim tare da Sipke Hulshoff a Leeuwarden bayan an kori Maas. A ranar 5 ga watan Junairu shekarar alif 2017, kungiyar kwallon kafa ta Cambuur ta sanar cewa Slot da abokin aikinsa Hulshoff zasu ci gaba da zama a matsayin su na masu bada horo a kungiyar saboda "bajintar da sukayi" a shekarar da kuma sanin makamar aiki.[7]
Slot da abokin aikinsa sun taimaki kungiyar kwallon kafa ta Cambuur domin fitar da kungiyar cikin halin da ta tsinci kanta daga mataki na 14 zuwa mataki na 3 a gasar lig. Sai dai sunyi rashin nasar tsallakawa a gasar Eridivisie sakamakon rashin nasara da sukayi a wasan tsallakewa gasar ta Eridevisie inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta MVV.
A gasar KNVB, Kungiyar ta samu nasarar zuwa matakin kusa da na karshe a karo na farko inda kungiyar kwallon kafa ta ajax tayi waje dasu. Saidai kungiyar kwallon kafa ta AZ tayi nasarar cin kofin da bugun daga kai sai mai tsaron raga.[8]
AZ
gyara sasheA shekarar alif 2017, Slot yabar Cambuur ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AZ inda yayi aiki a matsayin mataimakin mai bada horo a karkashin John Ban Den Brom. Mai kula da harkokin kasuwancin kungiyar ta AZ Max Huiberts ya kira Slot da "mai basira, mai hikima," AZ sun gama a mataki na 3 a shekarar alif 2018 sai kuma suka kare mataki na 4 a shekarar alif 2019.[9]
Kungiyar ta samu rashin nasara a wasan karshe a gasar kofin KNVB a shekarar 2018 inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Feyenood.
Ranar 10 ga watan Disamba 2018, an wallafa cewa "Arne slot shine babban kocin Kungiyar a shekarar alif 2019-20.
Slot ya zama mai bada horo na farko da ya samu nasarar lashe maki har guda 19 a cikin wasanni guda 8 da ya buga tare da kungiyar kwallon kafa ta AZ. A shekarar shi ta farko da kungiyar ya samu nasarar tsallakawa zuwa gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. Shekarar da ta dawo kuma, an soke gasar ta Eridevisie saboda cutar Covid19. A shekarar, kungiyar AZ ta gama ne a mataki na biyu a bayan kungiyar kwallon kafa ta Ajax inda kwallaye ne suka raba kunyoyin 2 duk da cewar ba'a bada kofin ba a shekarar. A shekara ta gaba, kungiyar kwallon kafa ta Dynamo Kyiv ce tayi waje da kungiyar a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai inda ta kare a mataki na 3 a cikin rukunin gasar. Kungiyar ta tsallaka zuwa gasar ƙasa da ta zakarun Turai wato gasar kajin Turai. Anan ne ta samu damar doke kungiyar kwallon kafa ta Napoli daci 1-0 inda nasarar ta zama tarihi a kungiyar ta AZ Standards.[10]
A ranar 5 ga watan Disamba 2020 an kori Slot daga Kungiyar akan rashin meda hankali a kungiyar inda suka fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord.
A lokacin kungiyar kwallon kafa ta AZ tana mataki na 7 a Teburi. A lokacin sa, Slot yana samun maki 2.11 duk wasa kuma hakan ya zama tarihin da bubu kocin da yayi abunda yayi.
Feyenoord
gyara sasheShekarar 2021-22
gyara sasheA ranar 15 ga watan Disamba shekara ta alif 2020 kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord tayi sanarwa cewa sun kammala yarjejeniya da Slot a matsayin mai horaswa na kungiyar inda ya fara aiki a shekarar alif 2021-22. da yarjejeniyar kwantiragi na shekara 2 sai dai akwai damar kara kwantiragin yakai shekara 3.
Slot yayi nasarar fahimtar salon wasa na Dick Advocaat wanda yabar kungiyar a mataki na 5 sannan cikin rukuni na buga gasar UEFA Europa League. Slot ya dauko hanyar gyara wajen gina kungiyar da samarin yan Kwallo. Slot ya samu goyon baya inda aka yarje mashi ya gina sabuwar kungiya da kuma salon wasansa. Marino Pusic mataimakin mai horaswa na farko da Robin Vanpersie (mai bada horo a fili) duk an sanyosu cikin mataimakan shi, saidai John De Wolf ya matsa a matsayin mai bada horo na 2.[11]
A shekarar Slot ta biyu kungiyar ta Feyenoord taje rukunin kungiyoyi 16 na gasar cin kofin Turai a karon farko tun bayan shekaru 20 inda suka gama a saman Alavia Parague, Union berlin da kuma Meccabi Haifa a cikin rukunin gasar UEFA Europa Conference League
A watan Fabrairu shekarar alif 2022, kungiyar Feyenoord suka kara ma Slot kwantiragi har zuwa shekara ta alif 2024. Kungiyar tayi nasarar kaiwa matakin karshe a gasar inda tayi awon gaba da kungiyar kwallon kafa ta Partizan, Slavia Parague da kuma Marseille. Kungiyar tayi rashin nasara a wasan karshe da ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Roma daci 1-0 a filin wasa na Tirana. A lig din gida kuma sun kare a mataki na 3 bisa Teburin Eridivisie. Hakan ya bashi damar lashe kyautar gwarzon kocin shekarar baki daya.[12]
Shekarar 2022-23
gyara sasheFarkon shekarar 2022-23 slot ya kara kwantiragin shi inda ya tsawaita shi har zuwa shekara ta alif 2025. Kungiyar ta Feyenoord ta cinye gasar UEFA Europa League inda ta hadu da kungiyar kwallon kafa ta Midtjylland, Lazio da Sturm Graz inda suka fito daga cikin rukunin tun shekarar 2002. Sun samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Shakhtar Donestk daci 7-1 a ranar 17 ga watan Maris shekarar alif 2023. Babbar nasarar kungiyar tun shekarar alif 1995.
Slot yasha gaban masu horaswa guda biyu masu tarihi a kungiyar inda yafi kowannensu samun nasara a wasannin gasar Turai inda yayi wasanni 15 ba tare da yayi rashin nasara ba.
Slot ya gama shekarar shi ta biyu a kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord da nasarar lashe gasar lig din a shekarar. Gasar farko a kungiyar tun shekarar alif 2016 da kuma 2017 a tarihin kungiyar. Anyi waje da kungiyar a gasar Europa League wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Roma a mataki na kusa da na kusan karshe. A gasar gida ta KNBV, sunyi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Ajax. A watan Mayu shekarar alif 2023 an fara alakanta mai horaswar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur a watan da zai kama. Sai dai kocin ya fito yace yana tare da kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord har ma ya kara kwantiragin shi har na tsawon shekara 1, inda kwantiragin zai kare a tsakiyar shekarar alif 2016. Slot ya samu nasarar lashe kyautar Michael Rinnus a matsayin gwarzon mai horaswa da yafi Kowa a shekarar. Kyautar an bada ta a watan June 2023. Inda ya zama mai horaswa na 4 da ya lashe gasar sau biyu a jere bayan Guus Hiddink, Frank De Boer da kuma Eric Ten Haag.[13]
Shekarar 2023-24
gyara sasheA shekarar alif 2023-24, anyi waje da kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord din daga gasar cin kofin Turai tun a wasannin rukuni. Sun kare na 3 a cikin rukunin. A cikin rukunin akwai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Lazio da kuma Celtic. Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Roma tayi waje da ita a gasar da bugun daga kai sai mai tsaron raga. Bayan buga wasan kungiyar kwallon kafa ta Roma, Slot yayi dai dai da tarihin Van Marwijk daya buga wasanni 36 na gasar Turai.
A ranar 21 ga watan Afrilu shekara ta alif 2024 Feyenoord sun samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta NEC a mataki na karshe inda suka samu nasarar lashe gasar kofin KNBV karo na 14. Mutane da yawa sun bayyana mai bada horon a matsayin kocin da ba'a taba yin Irin shi ba a kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord, saboda salon wasa da kuma samarin yan wasa da kuma tashe da kungiyar tayi.[14] Wasanshi na karshe tare da kungiyar a ranar 19 ga watan Mayu wasan da suka samu nasara daci 4-0 a wasan gida da abokan hamayya Excelsio Rotterdam. Inda suka kare suna tserayya da kungiyar kwallon kafa ta PSV.[15]
Liverpool
gyara sasheA watan Afrilu shekara ta alif 2024 an wallafa cewa kungiyar ta Premier League ta cinma matsaya da kocin na kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord. Kocin zai maye gurbin Jurgen Klopp a matsayin mai bada horo. Slot ya gazgata labarin a watan Mayu shekarar alif 2024.[16] A ranar 24 ga watan Mayu shekarar alif 2024, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tayi sanarwar kammala kulla yarjejeniya da mai horaswar. Slot zai zama mai horaswa a ranar 1 ga watan June shekarar alif 2024.[17]
Rayuwar Gida
gyara sasheSlot da matarshi Mirjam sunada yara guda 2."32"
Kididdigar Horarwa
gyara sasheKungiya | Nat | Daga | Har zuwa | Tarihi | Ref. | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Wasa | W | D | L | GF | GA | GD | Win % | |||||
Cambuur | 15 October 2016 | 30 June 2017 | 34 | 21 | 6 | 7 | 75 | 31 | +44 | 61.76 | ||
AZ | 1 July 2019 | 5 December 2020 | 58 | 32 | 16 | 10 | 118 | 52 | +66 | 55.17 | ||
Feyenoord | 1 July 2021 | 31 May 2024 | 150 | 98 | 29 | 23 | 344 | 150 | +194 | 65.33 | ||
Liverpool | 1 June 2024 | present | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | +0 | — | ||
Duka | 242 |
Girmamawa
gyara sasheDan wasa
Zwolle
Eerste Divisie: 2001–02, 2011–12
Mai horaswa
Feyenoord
Eredivisie: 2022–23[21]
KNVB Cup: 2023–24[36]
UEFA Europa Conference League runner-up: 2021–22[37]
Kyautar kai
Rinus Michels Award: 2021–22,[17] 2022–23[25]
Manazartar
gyara sashe- ↑ "Arne Slot: the overachiever and 'good guy' who can spark a revolution". Guardian. 26 April 2024. Retrieved 26 April 2024.
- ↑ Slot, van voetballer tot succescoach: 'Arne was jong en beetje eigenwijs'". nos.nl (in Dutch). 25 May 2022. Retrieved 18 September 2024
- ↑ "Slot: Paspoort" [Slot: Passport]. Voetbal International (in Dutch). Archived from the original on 13 February 2012
- ↑ 2023. Went, Rens (25 May 2022). "Slot, van voetballer tot succescoach: 'Arne was jong en beetje eigenwijs'" [Slot, from footballer to successful coach: 'Arne was young and a bit stubborn']. NOS.nl (in Dutch). Retrieved 23 April 2024.
- ↑ Vlietstra, Bart (26 April 2024). "Arne Slot: the overachiever and 'good guy' who can spark a revolution". The Guardian. London. Retrieved 15 September 2024.
- ↑ Went, Rens (25 May 2022). "Slot, van voetballer tot succescoach: 'Arne was jong en beetje eigenwijs'" [Slot, from footballer to successful coach: 'Arne was young and a bit stubborn']. NOS.nl (in Dutch). Retrieved 23 April 2024.
- ↑ "Cambuur schakelt Utrecht uit na strafschoppen" [Cambuur knocks Utrecht out after penalties]. NOS.nl (in Dutch). 26 January 2017. Retrieved 23 April 2024.
- ↑ "Assistent Slot komend seizoen nieuwe hoofdtrainer AZ" [Assistant Slot upcoming season new head coach AZ]. NU.nl (in Dutch). 10 December 2018. Retrieved 23 April 2024
- ↑ Someren, van, Jesse (30 September 2019). "Arne Slot beleeft recordstart bij AZ" [Arne Slot experiences record starts at AZ]. AD.nl (in Dutch). Retrieved 23 April 2024
- ↑ AZ verliest beste trainer in geschiedenis qua puntengemiddelde" [AZ loses best coach in history in terms of point average]. AD.nl (in Dutch). 5 December 2020. Retrieved 23 April 2024
- ↑ Arne Slot volgend seizoen nieuwe hoofdtrainer" [Arne Slot next season new head coach]. Feyenoord.nl (in Dutch). 15 December 2020. Retrieved 23 April 2024.
- ↑ "Trainer Slot verlengt contract bij Feyenoord tot 2025" [Coach Slot extends contract at Feyenoord until 2025]. NOS.nl (in Dutch). 24 July 2022. Retrieved 23 April 2024
- ↑ Dit Feyenoord-record evenaart Slot tijdens het duel met AS Roma" [Slot equals this Feyenoord record during the match against AS Roma]. VI.nl (in Dutch). 21 February 2024. Retrieved 23 April 2024
- ↑ 'Arne Slot: de trainer die 'sleeping giant' Feyenoord wakker maakte'" (in Dutch). Voetbalzone.nl. 28 April 2024. Retrieved 29 April 2024.
- ↑ Killen, Stephen (19 May 2024). "Arne Slot sent Liverpool message as final verdict given before Jurgen Klopp switch". Liverpool Echo. Retrieved 20 May 2024.
- ↑ "Arne Slot to become Liverpool FC's new head coach – Liverpool FC". www.liverpoolfc.com. 20 May 2024. Retrieved 20 May 2024.
- ↑ "Slot becomes first Liverpool manager this century to achieve Premier League feat". talkSPORT. 17 August 2024. Retrieved 25 August 2024.