Annette Mbaye d'Erneville
Annette Mbaye d'Erneville (an haife ta ashirin da uku ga watan 23 Yuni shekara 1926) marubuciya ce yar ƙasar Senegal. Ita ce mahaifiyar mai shirya fina-finai Ousmane William Mbaye, kuma ita ce batun fim dinsa na 2008, Mère-Bi.
An haife ta a cikin shekara 1926 a Sokone, Senegal, kuma ta yi karatu a gida, ta fara rayuwarta ta aiki a matsayin malami. A shekara 1947 ta tafi Faransa don karanta aikin jarida, kuma tun shekaran 1963 ta kasance mai aiki a gidan rediyon Senegal, ta zama Daraktan shirye-shirye. Har ila yau, ta kasance 'yar jarida mai kwarewa a kan batutuwan mata kuma cikin shekara 1963 ta kaddamar da mujallar bugu na farko na faransa ga matan Afirka. [1] Ta kware wajen rubuta adabin yara da wakoki kuma tana da alaƙa da Musée de la Femme Henriette-Bathily a Gorée.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Margaret Busby (ed.), Daughters of Africa: An International Anthology of Words and Writings by Women of African Descent, London: Jonathan Cape, 1992; Vintage, 1993, p. 330.