Anne Aasheim
Anne Aasheim (22 Afrilu 1962 - 30 Maris 2016) edita ce ƴar ƙasar Norway.
Anne Aasheim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Porsgrunn (en) , 22 ga Afirilu, 1962 |
ƙasa | Norway |
Mutuwa | 30 ga Maris, 2016 |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji) |
Ƴan uwa | |
Ahali | Erik Aasheim (en) |
Karatu | |
Harsuna | Norwegian (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida da editing staff (en) |
IMDb | nm8924578 |
Farkon rayuwa da Aiki
gyara sasheAn haife ta a Porsgrunn kuma ta fara aikin jarida a babban gidan jaridar birnin Varden a ƙarshen 1970s. Ta yi aiki a Dagen da Bergens Arbeiderblad kafin a dauke ta aiki a NRK Hordaland a 1988.[1]
Darekta
gyara sasheTa yi aiki a matsayin darekta na rikon kwarya a NRK P3 a Trondheim da NRK P2 a Oslo kafin a nada ta a matsayin darektan gidan labarai na Østlandssendingen a 1997. A shekarar 1999 ta yi aiki a matsayin mukaddashin darektan al'adu a kamfanin dillancin labarai, kafin ta zama darektan labarai na kasa da na gundumomi daga 2001 zuwa 2005. Bayan wani lokaci a matsayin babbar editan Dagbladet daga 2006 zuwa 2010, ta yi murabus kuma ta zama sabuwar manajan darakta na Majalisar Arts Norway a 2011.[1]
Iyali
gyara sasheTa yi aure da mai bincike Mette Tollefsrud, tayi rayuwa a Ila, Oslo.[2]
Dalilin Mutuwa
gyara sasheAasheim ta mutu sakamakon cutar kansar huhu a Oslo a cikin shekarar 2016.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Anne Aasheim". Store norske leksikon (in Norwegian). Retrieved 17 February 2014.
- ↑ Valle, Viggo; Mølster, Elisabeth Strand; Johansen, John Magne (19 January 2009). "Anne Aasheim" (in Norwegian). Norwegian Broadcasting Corporation. Retrieved 17 February 2014.
- ↑ "Anne Aasheim er død". 30 March 2016.
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |