Angelika Ouedraogo
Angelika Sita Ouédraogo (an haife ta a ranar 4 ga watan Disamba 1993) 'yar wasan ninkaya ce. Ta shiga gasar tseren mita 50 a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2012 inda ta zo ta 63 kuma ba ta kai matakin wasan kusa da na karshe ba.[1][2][3][4]
Angelika Ouedraogo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ouagadougou, 4 Disamba 1993 (30 shekaru) |
ƙasa | Burkina Faso |
Karatu | |
Makaranta |
International Institute for Water and Environmental Engineering (en) Georgia Southern University (en) Oklahoma State University–Stillwater (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | swimmer (en) da modern pentathlete (en) |
Mahalarcin
| |
Nauyi | 63 kg |
Tsayi | 170 cm |
Ouedraogo ta shiga gasar tseren mita 50 a gasar Olympics ta bazara ta 2016 inda ta zo ta 67 kuma ba ta tsallake zuwa matakin kusa da na ƙarshe ba.[5] Ta kasance mai riƙe da tutar ƙasarta a yayin bikin rufe gasar.[6]
A shekarar 2019, ta wakilci Burkina Faso a gasar cin kofin ruwa ta duniya na 2019 da aka gudanar a Gwangju, Koriya ta Kudu. Ta fafata ne a gasar tseren salo na mita 50 na mata.[7] Ba ta samu damar shiga wasan kusa da na karshe ba.[7]
Ouedraogo ta sake shiga gasar tseren mita 50 a gasar Olympics ta bazara ta 2020 inda ta kasance a matsayi na 58 gaba ɗaya kuma ba ta tsallake zuwa matakin kusa da na ƙarshe ba.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Sports Reference profile
- ↑ London 2012 profile Archived 21 ga Yuli, 2012 at the Wayback Machine
- ↑ L'Observateur Paalga Jeux olympiques : Sévérine Nébié, l'espoir burkinabè Archived 26 Disamba 2013 at the Wayback Machine 29 July 2012 "Des onze membres qui composent la délégation burkinabè, on compte cinq athlètes : Sévérine Nébié (judo), Gérard Kobeané, Marthe Koala (Athlétisme), Angelica Ouédraogo et Adama Ouédraogo (natation)."
- ↑ Sidwaya Les 22 meilleurs sportifs du Burkina qui fêteront les 20 ans de l'AJSB Archived 26 Disamba 2013 at the Wayback Machine Assemblée générale de l'AJSB 25 November 2012 "Angélica Ouédraogo qui a dit n'avoir plus d'adversaire au Burkina en natation, a convaincu les journalistes sportifs."
- ↑ "Rio 2016". Rio 2016. Archived from the original on 22 September 2016. Retrieved 22 August 2016.
- ↑ "The Flagbearers for the Rio 2016 Closing Ceremony". 21 August 2016. Retrieved 22 August 2016.
- ↑ 7.0 7.1 "Women's 50 metre freestyle – Heats – 2019 World Aquatics Championships" (PDF). 2019 World Aquatics Championships. Archived (PDF) from the original on 26 July 2020. Retrieved 26 July 2020.
- ↑ "Women's 50m Freestyle results at the 2020 Summer Olympics". Archived from the original on 31 July 2021. Retrieved 30 July 2021.