Anamero Sunday Dekeri dan majalisar wakilan Najeriya ne mai wakiltar mazabar tarayyar Etsako a Najeriya.

Anamero Sunday Dekeri
Rayuwa
Haihuwa 25 Oktoba 1969 (54 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Anamero Sunday Dekeri a kauyen Ogute-Oke, Okpella, Jihar Edo, Najeriya. Iyalinsa sun yi aiki a matsayin manoman makiyaya. Dekeri ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar firamare ta Ugbedudu, sannan ya samu takardar shaidar kammala karatunsa na sakandare a makarantar Ogute-Oke. Daga nan ya ci gaba da samun digiri na farko a fannin shari’a a Jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma. Sannan kuma tsohon jami'in 'yan sanda ne dake Ikeja.[1]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. "Distribution of Wheel Chairs in Edo North". Anamero. Retrieved 16 January 2024.