Amirul Hajji shi ne shugaban alhazai, wanda hukumar gwamnati ko hukumar Hajji ko shugaban addini ta naɗa.

Amirul Hajj

Ayyuka gyara sashe

Ayyukan Amirul Hajji sun haɗa da tafiyar da aikin hajji, nasiha da sharuɗɗan da suka dace da aikin Hajji, da jagorantar sallah, da kula da korafe-korafe.

Fitattun Mutane gyara sashe

  • Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III shi ne Amirul Hajj na 'yan Najeriya masu aikin Hajji na shekarar 2013.
  • Ga al'ummar Dawudi Bohra, Mufaddal Saifuddin shi ne Amirul Haj a shekarar 2012, da dan uwansa Malik ul Ashtar Shujauddin a shekarar 2019.
  • An nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Abba Musa Rimi a matsayin Amirul Hajj ga Musulman Najeriya a watan Agustan 2013.[1][2]

Manazarta gyara sashe

  1. "NAHCON says Sultan remains permanent Amirul Hajj". Premium Times. 28 June 2013. Retrieved 14 March 2014.
  2. "Katsina Appoints Rimi as Amirul-Hajj". Daily Times of Nigeria. 15 August 2013. Retrieved 14 March 2014.