Aminata Ouédraogo
Aminata Ouédraogo 'yar fim ce kuma mai kula da harkokin fina-finan Burkinabe. Ita ce babban jami'in gudanarwa na kungiyar mata ta Pan-African Women in the Image Industry (UPAFI). [1]
Aminata Ouédraogo | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Burkina Faso |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ouagadougou |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta |
Mamba | Panafrican Film and Television Festival of Ouagadougou |
Rayuwa
gyara sasheOuédraogo tayi karatu a Institut Africain d'Education Cinématographique (INAFEC), makarantar fina-finai a Jami'ar Ouagadougou, kafin ta yi karatu a Institut du Multimedia et Architecture de la Communication (IMAC) a Paris. [1]
Ouédraogo ta shawarci Panafrican Film and Television Festival of Ouagadougou (FESPACO). A shekarar 1991, a FESPACO karo na 12, ta kirkiro kungiyar kwararrun mata na Afirka a Cinema, Talabijin d nea Bidiyo (AFAPCTV).[2] A cikin shekarar 1995 an sake fasalin AFAPCTV a matsayin Ƙungiyar Mata ta Afirka ta UPAFI, tare da Ouédraogo a matsayin babbar mai gudanarwa.[3] Ita ce mai ba da shawara ta fasaha ga ministar al'adu da yawon shakatawa a Burkina Faso.[3]
Filmography
gyara sashe- L'impasse, 1988. Fiction.
- A qui le tour?, 1991. Documentary
- Ak Patashi (Qui m'a poussé), 1992. Documentary.
- Alcoolisme, 1992. Documentary.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 'Interview with Aminata Ouédraogo', in Ellerson, Beti, ed., Sisters of the Screen: Women of Africa on Film Video and Television, NJ: Africa World Press, 2000. Reprinted online at https://www.africanwomenincinema.org/AFWC/Ouedraogo.html Archived 2020-11-06 at the Wayback Machine.
- ↑ Sophie Hoffelt (1998). "Les femmes réalisatrices en Afrique subsaharienne". L'Afrique politique: 24. ISBN 978-2-86537-843-2.
- ↑ 3.0 3.1 Claire Diao, Aminata Ouedraogo : « Un jour, une femme remportera l’Étalon de Yennenga ! », africultures, 2 June 2009.