Aminata Diallo Glez
Aminata Diallo Glez (an haife ta a shekara ta 1972) 'yar wasan fim ce, 'yar wasan kwaikwayo, kuma furodusa wanda kuma aka fi sani da Kadi Jolie. [1]
Aminata Diallo Glez | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bani (en) , 1972 (52/53 shekaru) |
ƙasa | Burkina Faso |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Damien Glez (en) |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta da filmmaking (en) |
IMDb | nm0224503 |
Rayuwa
gyara sasheAn haife ta a Dori, Burkina Faso, Aminata Diallo ɗaya ce daga cikin yaya tara da mahaiin su Hassane Diallo ya haifa, likitan dabbobi, da Mandy Togoyéni. Ta yi fatan zama likita tun tana yarinya, amma mahaifinta ya rasu a shekara ta 1983, lokacin tana makarantar sakandare. Ta ci gaba da karatunta a Wemtenga, gundumar Ouagadougou. Bayan haɗuwa da Théâtre de la fraternité, ƙungiyar wasan kwaikwayo na Jean-Pierre Guingané, ta shiga ƙungiyar bayan makaranta. Maimakon ta sami wurin yin nazarin ilimin harshe a Jami'ar Ouagadougou, ta zama 'yar wasan kwaikwayo na cikakken lokaci, tare da Théâtre de la fraternité. [1]
A farkon shekarun 1990 Fanta Regina Nacro ta ka ta rawar gani a fim ɗin Puk-Nini, wanda ta fara sabuwar sana'ar Diallo a matsayin 'yar wasan kwaikwayo ta allo. A matsayinta na babbar jarumar shirye-shiryen talabijin Kadi jolie, ta sami mabiya a faɗin Afirka. [1]
Ta fara nata kamfanin samar da TV, Jovial Productions, wanda ya samar da jerin abubuwan ciki har da 'Trois hommes, un village' (wanda ya lashe Mafi kyawun Series a FESPACO 2005), Trois femmes, un village da Super flicks (ko Marc da Malika ). A shekara ta 2006 ta kuma kafa wani art festival, "Fet' Arts". [1]
Ta auri Damien Glez, mai zane-zane na Jeune Afrique. [2]
Na ɗan lokaci ta yi ritaya daga rayuwar jama'a don kula da mahaifiyarta, wacce ke da ciwon daji, [3] kuma wacce ta mutu a shekarar 2019. [4]
Filmography
gyara sasheForudusa
gyara sashe- Super flicks (2008)
- Trois femmes, un village (2009)
Yar wasan kwaikwayo
gyara sashe- Puk Nini de Fanta Régina Nacro (1996) as Ada
- Conseils d'une tante d'Idrissa Ouedraogo (2001) as Kadi Jolie
- Kadi Jolie d'Idrissa Ouedraogo (2001) as Kadi Jolie
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Aminata Diallo Glez: Itinéraire d’une comédienne sans fard, LeFaso.net, 31 December 2009. Accessed 30 July 2020.
- ↑ Qui est Damien Glez, le caricaturiste de Jeune Afrique?, Press Afrik, 29 January 2016. Accessed 30 July 2020.
- ↑ Burkina Faso: la triste histoire de Kadi Joli (Aminata Diallo Glez) Archived 2023-07-22 at the Wayback Machine, L-DRII, 2 September 2019. Accessed 30 July 2020.
- ↑ Daouda Zongo, Nécrologie: inhumation de la mère de Kadi jolie au cimetière de Gounghin ce mardi, Wakat Séra, 15 October 2019. Accessed 30 July 2020.