Farfesa Amina Abubakar Bashir (An haife ta ranar 8 ga watan Yuli, shekarata alif 1960), ta kasance Bakarkariya ce 'yar asalin garin Daya dake karamar hukumar Fika amma ta taso ne a garin Potiskum, Jihar Yobe, Najeriya. Malamar jami'a ce, masaniyar harshen Turanci kuma farfesa. Ta shahara ne bisa kasancewarta mace ta farko da ta fara zama farfesa a tarihin jihar Yobe. [1]

Marigayi Alhaji Garba Daya, Hakimin Daya kuma Madakin Fika, shine mahaifinta, mahaifinta masani ne kan magunguna. Ya yi karatun haɗa magunguna, kuma jigo a ƙungiyar masu haɗa magunguna ta Arewacin Najeriya. Bayan ya yi ritaya ne sai ya buɗe masana’antar haɗa magunguna mai suna Daya Pharmacy. Ya rasu ranar 7 ga watan Mayu a shekarar 2022 an kuma binne shi (Jana'izarsa) ranar 8 ga watan Mayu shekarar 2022.[2]

Farfesa Amina ta fara firamare a Central Primary School, da ke Nguru. Ta kuma sake shiga firamaren St. Patrick Primary School, wata makaranta mallakin Missionary School, firamare mafi daraja a garin Maiduguri, a lokacin da a ka yi wa mahaifinta canjin wurin aiki zuwa birnin Maiduguri, nan dai aka sake sauya wa mahaifinta wurin aiki inda ta samu nasarar kammala makarantar farko, Firamarenta a Damboa da ke garin Potiskum, bayan nan, ta kuma samu izinin karatu a kwalejin ƴan mata da ke Maiduguri, inda ta samu shaidar kammala sakandari a shekarar 1977.[3]

 
Farfesa Amina BashirTa zama Farfesa ne a shekarar 2009, wacce a tahirin jihar Yobe ita ce mace ta farko da ta kai wannan matsayin.

Kasantuwarta wacce ta fito daga zuri’ar da suka san muhimmancin ilimi, suke baiwa ilimi gayar muhimmanci, ba su bari ta zauna wani zaman kashe wando ko zaman jiran wani abu ba, nan take suka antaya ta zuwa Kwalejin nazarin ilimin kimiyya da sauran darussa da ke Mubi a jihar Adamawa, gabanin ta samu izinin shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke a Zariya.[4]

Ta samu nasarar kammala jami’ar ABU ne a shekarar 1981, inda ta yi digiri ɗinta kan darasin harshen nasara wato Ingilishi. Koda wasa ba ta zauna zaman wani abu ba, ta daura karatunta domin neman digiri na biyu wato ‘Masters’, inda kuma ta karanci ilimi koyarwa, a jami’ar Maiduguri, kana ta yi digirin-digirgir wato PhD a kan harshen Ingilishi (English Sociolinguistics) a jami’arta da ta yi a farko wato Ahmadu Bello Unibersity, Zaria.

Farfesa Amina Bashir ta fara aikinta ne tun a shekarar 1982 gabanin ma ta je ta yi wa ƙasa hidima, ta yi aiki a jami’ar Maiduguri ta yi aiki sosai a matsayin mai ilimi matakin digiri na biyu, sannu a hankali har ta zama shugaban tsangayar koyar da ilimin Turanci (English) na jami’ar Maiduguri a shekarar 2010, har ta kai matsayin farfesa domin ta aikatu sosai a wannan lokacin. Hakanan ta bar aiki a jami’ar Maiduguri kana ta tafi jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, a tsakanin 2013 zuwa shekarar 2015 ta sake zama shugaban tsangaya a jami’ar Dutse, wacce har ta kai matsayin mataimakiyar shugaban jami’ar (Deputy Vice Chancellor), a shekarar 2016 ne ta zama shugaban sashin ilimin zamantakewa (Dean, Faculty of Arts and Social Sciences, Federal University Dutse) a jami’ar Dutse har zuwa yau tana kan wannan kujerar.

Gudummawa

gyara sashe

Farfesa Amina Bashir ta shahara gaya, ta kai matsayin da ta ziyarci jami’o’i daban-daban da wurare daban-daban, ta takara rawar gani sosai wajen ci gaban ilimi. Daga cikin jami’o’in da ta ziyarta hadi da bayar da gudunmawa a matsayinta na Farfesa sun haɗa da Jami’ar BUK da ke Kano a shekarar 2014, Jami’ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sokoto a tsakanin (2014 zuwa 2016), Jami’ar ƴan sanda da ke Wudil a tsakanin (2016 zuwa 2017) da kuma jami’ar jihar Yobe daga shekarar 2017 har zuwa yau.

Ta zama kwararriya kan fannin koyarwa, ta goge sosai, ta shafe shekaru sama da 35 tana koyarwa, kana tana kuma bincike da nazari a jami’o’i daban-daban. Ta wallafa littafai guda 3, makaloli da mujallu sama da 40 wacce take gabatarwa a jami’o’i daban-daban, ta zama editan mujallu daban-daban a tarihin rayuwarta.

Karramawa

gyara sashe

Farfesa ta amshi lambobin yabo masu tarin yawa a rayuwarta, kama daga wajen ɗalibai, ƙungiyoyi, gwamnatoci da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu, a bisa haka lifafarta ya cilla inda ta zama tauraruwa a cikin mata ba ma a jihar Yobe kaɗai ba har da shiyyar Arewa Maso Gabas gaba ɗaya.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://hausa.leadership.ng/hajiya-amina-bashir-daya-mace-ta-farko-da-ta-zama-farfesa-a-jihar-yobe/amp/
  2. https://aminiya.dailytrust.com/farfesa-amina-bashir-yadda-na-yi-gwagwarmayar-shekara-30-ina-koyarwa
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-03-04. Retrieved 2022-05-25.
  4. https://myschoolnews.com.ng/index.php/amina-bashir-first-female-professor-from-yobe-state/17564[permanent dead link]